31
May
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara ɗaya a kan karagar mulki bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayun 2023 a matsayin Shugaban Nijeriya. Ƙasar da ta kwashe shekaru tana fama da matsalar tsaro a kusan dukkanin yankunanta shida. Duk da cewa al'ummar yankunan da aka fi fama da matsalar tsaron sun yi fatan a samun sa’ida bayan karɓar sabuwar gwamnati, amma wasu na ganin cewa matsalar tamkar ƙara muni ta yi. An ci gaba da fuskantar matsalar masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da yi wa mutane…