Tinubu ya sa zamowar Osimhen Gwarzon Afirka a nasarorinsa na shekara guda

Daga MAHDI M. MUH’D

Tinubu ya saka nasarar da Osimhen ya samu na zama gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka a cikin nasarorin da ya samu yayin da ya cika shekara guda a kan karagar mulki.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya ɗan wasan gaba na Napoli Victor Osimhen ya zama gwarzon ɗan ƙwallon Afrika na bana a matsayin wani ɓangare na nasarorin da ya samu yayin da ya cika shekara guda a kan karagar mulki.

Idan za a iya tunawa, Osimhen ya zama gwarzon ɗan ƙwallon Afrika na 2023 bayan ya doke Mohamed Salah da sauran su, inda ya zama ɗan Nijeriya na farko da ya lashe kyautar tun Nwankwo Kanu a 1999.

Osimhen, mai shekara 25, ya zura ƙwallaye 26 a raga yayin da ya taimakawa Napoli ta yi nasara a gasar Seria A a bara kuma shi ne kan gaba wajen zura ƙwallo a raga a gasar ta Italiya.