Gwamnan Zamfara ya jajirce kan ƙin sulhu da ‘yan bindiga duk da ci gaba da garkuwa da dattawa 50

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An yi garkuwa da dattawan ƙauyen Magamin Diddi a Ƙaramar Hukumar Maradun a farkon watan Yuni akan abin da majiyoyi suka bayyana a matsayin sa kai domin sulhu da dabar sanannen jagoran ‘yan bindiga, Jammo wanda aka ce shi ke da ikon gudanar da yankin dajin Muntsira.

Bincike sun nuna cewa dattawan sun shirya ne da nufin zuwa tattaunawar sasanci da jagoran ‘yan bindigar da kuma ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da za su ba mazauna yankunan damar gudanar da harkokinsu na noma cikin aminci ba tare da fargabar wani hari ba.

Saidai, a madadin karɓar wannan tayi, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da dattawan su guda 50 a sa’ilin da suak je tattaunawar.

Wannan al’amari ya haifar da yamutsi a sassan jihar, inda da dama daga mazauna suka caccaki ƙarfin ‘yan bindigar da kuma abin da suka kira da gazawar gwamnati wajen kawo ƙarshen ta’addanci.

Haka kuma, cigaba da zama a komar ‘yan ta’addar da dattawan ke yi ya ƙara nuna yadda al’amarin rashin tsaro a jihar da shiyyar Arewa maso Yamma ke ƙara taɓarɓarewa.

To saidai duk da wannan hali, Gwamna Dauda Lawal na jihar ya nesanta gwamnatinsa daga yunƙurin dattawan, yana mai bayyana hakan a matsayin “haramtacce kuma wanda aka yi ba da yawun gwamnati ba”.

A cewarsa, gwamnatinsa na gudanar da bincike mai zurfi akan al’amarin, inda ya kuma soki dattawan akan yadda suka ɗauki matakin tattaunawar ba tare da sanar da hukumomin gwamnati ba.

Da yake jawabi a wata hira da BBC Hausa, Gwamna Lawal ya bayyana rashin jin daɗinsa akan matakin nasu, yana mai ƙalubalantar dukkan wanda zai ɗauki irin matakin ba tare da amincewar gwamnati ba.

Kazalika, ya jaddada matsayar gwamnatinsa na ƙin amincewa da sulhu da ‘yan bindiga a matsayin hanyar shawo kan matsalolin tsaro da suka haɗa da garkuwa da mutane, kashe-kashe da sauran manyan laifuka a jihar.

By Babaji

Leave a Reply