Wani mutum da ake zargin yana safarar makamai ya ɓace ɓat bayan karɓar Naira miliyan 95 daga hannun wani fitaccen jagoran ’yan bindiga a Jihar Katsina, da sunan zai saya masa manyan makamai.
Rahotanni sun ce zargin ya fito ne daga ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Musawa/Matazu, Abdullahi Aliyu, wanda aka fi sani da Janar, yayin wata hira da ya yi da NTA Hausa.
A cewarsa, mutumin ya karɓi kuɗin ne daga wani shugaban ’yan bindiga da ke aiki a ƙaramar hukumar Matazu, bayan ya yi masa alƙawarin samar masa da manyan makamai. Sai dai bayan karɓar kuɗin, ana zargin ya tsere ba tare da cika alƙawarinsa ba.
Rahotannin sun ce lamarin ya haifar da fargaba a wasu yankunan Matazu, inda har yanzu ƙungiyoyin ’yan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na daƙile matsalolin tsaro.
Abdullahi Aliyu ya kuma bayyana cewa lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake fuskantar sabbin matsalolin tsaro, bayan rahotannin cewa fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Maha, ya janye daga yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi da wasu ƙauyuka.
Ya ce tun bayan hakan, shugaban ’yan bindigar ya ƙaƙaba haraji mai tsanani kan dabbobin al’ummomin yankin, abin da ya ƙara jefa mazauna yankin cikin wahala tare da ƙara fargabar yiwuwar sabbin hare-hare.
Rahoton ya kuma nuna cewa wannan zargin na damfarar Naira miliyan 95 ya sake fito da yadda ake mu’amala tsakanin masu aikata laifuka, inda ake zargin mutumin da ya karɓi kuɗin ya tsere ba tare da isar da makaman da aka yi alƙawari ba.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatar da faruwar lamarin ko kuma sanar da fara bincike kan zargin.
.
