Gwamnatin Kano ta cafke likitan bogi yana yin magunguna marasa inganci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi likitan bogi ne, bisa zargin raba magungunan da ba su samu amincewar hukumomi ba tare da gudanar da wani shirin ba da magani ga jama’a ba tare da izini ba a yankin Panshekara.

An kama wanda ake zargin ne a wani samame na haɗin gwiwa da jami’an Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, da Hukumar Kula da Asibitoci Masu Zaman Kansu ta Jihar Kano (PHIMA), da Cibiyar Daƙile da Yaɗuwar Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) tare da Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya, bayan samun bayanan sirri kan ayyukansa.

A cewar Ma’aikatar Lafiya, ana zargin mutumin ya fito ne daga Jihar Nasarawa, inda ya tara ɗaruruwan mutane, sannan ya riƙa zuba wasu sinadarai a bakunansu da idanunsu ba tare da ya fara yi musu wani binciken lafiya ba, ko samun izinin hukumomin lafiya masu ruwa da tsaki.

Ma’aikatar ta kuma ce ana zargin ya raba wani koren ruwa yana iƙirarin cewa yana warkar da cututtuka fiye da 100, tare da karɓar kuɗi daga jama’ar da suka halarci shirin.

Jami’an lafiya sun bayyana cewa mazauna yankin ne suka sanar da KNCDC da PHIMA game da lamarin, abin da ya sa aka shirya samamen da ya kai ga cafke wanda ake zargin tare da ƙwace magungunan da sauran kayayyakin da ake amfani da su.

Da yake mayar da martani, Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan nasara ta nuna ƙudirin gwamnati na kare al’umma daga masu yaudara da kuma ayyukan jinya da ke barazana ga lafiyar mutane.

Ya buƙaci jama’a su kasance masu sa ido, tare da gaggauta kai rahoton duk wanda ya yi ƙarya a matsayin ma’aikacin lafiya ko kuma ke gudanar da ayyukan jinya masu cike da shakku ga hukumomin da suka dace.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma da na unguwanni da su riƙa sanya ido kan irin waɗannan ayyuka a yankunansu, yana mai jaddada cewa duk wani shirin rabon magunguna ko ba da kulawar lafiya kyauta dole ne ya bi hanyoyin da gwamnati ta tanada.

Ya yi gargaɗin cewa shirya gangamin raba magunguna ga jama’a, ko na zamani ko na gargajiya, ba tare da sahalewar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ba, laifi ne da doka ta tanadi hukunci a kansa.

By ukarofi

Leave a Reply