
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sabon kociyan Real Madrid ta Ƙasar Sifaniya, Jose Mourinho, ya samar da wasu dokoki guda huɗu da nufin dawo da ɗa’a, ƙwarewa da haɗin kai acikin ‘yan wasan ƙungiyar.
A cewar jaridar Sifaniya AS, ɗan ƙasar Portugal ɗin mai shekaru 63 ya gano wasu ɗabi’u da yake ganin akwai buƙatar a sauya su tun bayan dawowarsa Bernabeu.
Kocin ya samar da sababbin tsarin gudanarwa akan cin abinci, tsare aiki, gyaran tsarin kula da lamuran raunin ‘yan wasa sa kuma dunƙule tawagar ‘yan wasa.
A sabon wa’adin nasa, ‘yan wasan Real Madrid za su kasance masu taƙaitaccen ‘yanci kan lamuran abinci, inda ƙungiyar ce za ta riƙa tsara musu abinci ciki har da karin kumallo da ababen marmari. An shirya haka ne da manufar abincin da ‘yan wasa suke ci t dace da ƙwazonsu da shiryawa ta zahiri yayin fuskantar wasanni.
Haka kuma, an sanya dokar hana zuwa wajen horo latti, inda aka tsara hukunta dukkan wanda aka samu da aikata laifin, zai fuskanci yin atisaye shi kaɗai a madadin shiga sahun sauran ‘yan wasa.
Haka kuma, wajibi ne kowane ɗan wasa ya je filin atisaye sa’a guda kafin fara gudanar da ababen da jaddawalin atisayen ya ƙunsa.
Kazalika, Mourinho ya mayar da tsarin karɓar magani daga samun rauni na bai-ɗaya ta yadda duk ɗan wasan da yake ƙoƙarin warkewa daga rauni zai riƙa karɓar horo bisa sanya idon jami’an lafiya da ƙwazo na ƙungiyar.
