Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU, Jos
Malaman addinin Musulunci da fastoci 20 ne suka samu horo kan yadda za su kaucewa yaɗa bayanan da basu inganta ba, da yaɗa labaran ƙarya cikin koyarwar su.
Malaman sun shafe tsawon yini biyu ne suna samun wannan horo daga jami’an cibiyar yaƙi da yaɗa labaran ƙarya ta alƙalanci, wanda suke samun tallafin ma’aikatar kula da harkokin ƙasashen waje ta Birtaniya (FCDO/ISF), ƙarƙashin cibiyar ba da horo kan harkokin watsa labarai da ilimin sadarwa ta Initiative for Media Development and Information Literacy.
A cewar jagoran cibiyar alƙalanci, Malam Alhassan Bala, ɗan jarida mai nazari kan harkokin da suka shafi yaɗa labaran ƙarya, “Wannan shiri ne na ƙoƙarin yaƙi da labaran ƙarya daga tushe. Saboda malaman addini su ne jagororin al’umma, idan wasu lokuta suna faɗawa tarkon masu yaɗa labaran ƙarya su faɗi wani bayani wanda ba daidai yake ba, ko kuma daga baya a gano ba gaskiya ba ne, a cikin karatuttukan su da koyarwar su, hakan na da illa sosai ga kimar su da kuma tasirin maganganunsu a wajen mabiyansu da sauran jama’a.”
Wakilin ofishin jakadancin Birtaniya a Nijeriya kuma ƙwararre kan illolin yaɗa bayanan ƙarya, Oriola Odotoye, wanda ya shaida yadda taron ya gudana, ya bayyana cewa, wannan tallafi ya samo asali ne ƙarƙashin wani shirin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin Birtaniya da Nijeriya game da yaƙi da yaɗuwar bayanai marasa inganci da farfagada.
An zaɓo mahalarta taron ne daga ɓangaren Musulmi a ƙarƙashin ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) da kuma ƙungiyar haɗin kan Kirista ta CAN, inda kowanne ɓangare ya wakilta mutane goma.
A yayin wannan bita, an tattauna kan muhimman batutuwa da suka shi muhimmancin tantance bayanai, karɓar bayanai daga sahihan mutane ko wata kafa mai inganci, da hanyoyin yaƙi da matsalolin da labaran ƙarya da farfagada ke haddasawa a cikin al’umma da sauran su.
Wakilan ƙungiyoyin addinin Musulunci da Kirista sun gabatar da nasu laccocin da a ciki suka ja hankulan malaman addini da al’umma kan muhimmancin riƙo da koyarwar addini kan yaɗa labaran ƙarya.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun yabawa Cibiyar Alƙalanci da waɗanda suka ɗauki nauyin horarwar kan bisa ilimin da suka ba su, wanda suka ce sun samu ƙarin wayewa game da hanyoyin yaƙi da labaran ƙarya da yadda jita-jita ke yaɗuwa a cikin jama’a, da kuma nauyin da ke kansu a matsayin su na jagororin al’umma, don ilimantar da mabiyansu.
