
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF), ta taya Mista Samson Adamu bisa tabbatar da shi a ranar Alhamis a matsayin Babban Sakatare Janar na Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF).
Wannan tabbaci ya sa Adamu, wanda ya shiga wata hukumar ƙolin ƙwallon ƙafa da ke Cairo, a matsayin Daraktan Gasa, shi ne ɗan Nijeriya na farko da ya zama babban jami’in gudanarwa a tarihin CAF na tsawon shekara 70.
Sakataren riƙo na NFF, Dakta Emmanuel Ikpeme MON a wata wallafa, ya ce “Wannan labari ne mai daɗi. Ina mai matuƙar farin ciki ga Samson Adamu bisa tabbatar da shi kuma na san zai sanya Nijeriya da Afirka alfahari.” A cewarsa, yana da ilimi da ƙwarewa a fannin ƙwallon ƙafa don haka ake masa fatan sauke nauyin da aka ɗora masa bisa inganci, yana mai cewa NFF za ta ba shi dukkan goyon bayan da ake buƙata.
Bayan aiki a matsayin Daraktan Gasa a CAF, an taɓa naɗa Adamu a matsayin Daraktan Gasa da Taruka. A ranar 29 ga Maris, 2026 ne aka naɗa shi a matsayin sakataren CAF na riƙo bayan ɗan Kongo mazaunin Switzerland, Veron Mosengo-Omba ya yi murabus daga muƙamin.
