Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya mayar da martani ga masu sukar gwamnatin sa kan ci gaba da karɓar basussuka daga ƙasashen waje, musamman shugabannin jam’iyyun adawa. Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda ake amfani da kuɗaɗen wajen gina ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar ’yan ƙasa, ba wai yawan kuɗin da aka karɓa a matsayin bashi ba.
A wani rubutu mai taken “Daga Sauye-sauyen Tattalin Arziki zuwa Aiwatar da Manufofi: Dabarun Zuba Jari a Ababen More Rayuwa da Bunƙasa Tattalin Arziki”, Tinubu ya bayyana cewa ya kamata a auna nasarar karɓar bashi ne da irin ayyukan da aka gudanar da kuɗin, ƙimar da aka samar da kuma makomar da aka tanadar wa al’ummar Nijeriya.
An bayyana matsayin shugaban ƙasar a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mai Ba Shi Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa, Bayo Onanuga, mai kwanan wata 29 ga Oktoba, 2026. Tinubu ya rubuta cewa, “Babbar tambayar ba ita ce yawan kuɗin da muke aro ba, sai dai abin da muke ginawa, ƙimar da muke samarwa da kuma makomar da za mu bari a baya.”
Shugaban ƙasar ya lissafa manyan ayyukan more rayuwa da gwamnatinsa ke ganin za su ƙarfafa ƙarfin samar da kayayyaki da ayyuka a Nijeriya. Daga cikinsu akwai Babbar Hanyar Gaɓar Teku ta Legas zuwa Kalaba, Babbar Hanyar Sakkwato zuwa Badagry, Babbar Hanyar Trans-Sahara, gyaran hanyoyin sadarwar lantarki da kuma zamanantar da manyan tashoshin jiragen ruwa na kasuwanci da ke Legas.
Ya ce waɗannan ayyuka, tare da zuba jari a fannonin kiwon lafiya, ilimi da koyon sana’o’i, za su haɗa yankunan tattalin arziki, rage kuɗin jigilar kayayyaki, buɗe hanyoyin bunƙasa noma da masana’antu, tare da jawo hankalin masu zuba jari daga kamfanoni masu zaman kansu.
A cewar Tinubu, ana sa ran Babbar Hanyar Gaɓar Teku ta Legas zuwa Kalaba za ta rage kuɗin jigilar kayayyaki a yankin da kashi 15 zuwa 20 cikin 100. Haka kuma, ana hasashen aikin zai iya taimakawa wajen ƙara yawan tattalin arzikin Nijeriya da kusan kashi biyu cikin 100, sakamakon faɗaɗa kasuwanci, yawon buɗe ido da ayyukan masana’antu.
Ya ce ana kuma sa ran aikin zai samar da guraben ayyukan yi kai tsaye kusan 100,000 a fannonin gine-gine da injiniyanci, tare da samar da wasu guraben ayyukan yi sama da 150,000 a kaikaice, musamman a fannonin jigilar kayayyaki, samar da kayan gini da sauran ayyukan da ke da alaƙa da aikin. Shugaban ƙasar ya jaddada cewa, “Ba manyan hanyoyi kawai muke ginawa ba. Muna buɗe sabbin hanyoyin bunƙasa tattalin arziki, haɗa kasuwanni, buɗe ƙofofin masana’antu da kuma sauya tsarin da tattalin arzikin Nijeriya yake gudana a cikinsa.”
Tinubu ya bayyana cewa burin gwamnatinsa na mayar da tattalin arzikin Nijeriya ya kai darajar dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030 ba zai tabbata ba tare da ci gaba da zuba jari a ababen more rayuwa ba. Ya ce ana buƙatar ingantattun hanyoyi da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa domin ƙara yawan abin da ake samarwa, bunƙasa masana’antu da faɗaɗa cinikayya. Ya ce, “Ba za mu iya gina tattalin arzikin da darajarsa ta kai dala tiriliyan ɗaya da ababen more rayuwar da aka tsara domin tattalin arziki mai ƙarancin girma ba.”
Shugaban ƙasar ya ce wasu alamomin tattalin arziki da suka inganta, tare da ƙaruwa da amincewar masu zuba jari na ƙasashen duniya, sun buɗe wa Nijeriya ƙofofin jawo jari na dogon lokaci da faɗaɗa muhimman ayyukan more rayuwa. Ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara a watan Mayun 2023 sun taimaka wajen dawo da daidaito a manyan sassan tattalin arziki, warfafa kuɗaɗen gwamnati da kuma inganta matsayin Nijeriya a kasuwannin hada-hadar kuɗi na duniya.
Tinubu ya jaddada cewa ba za a iya cimma burin tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya ta hanyar shela kawai ba. Ya ce dole ne a gina shi ta hanyar zuba jari mai ɗorewa, ƙara yawan abin da ake samarwa, bunƙasa masana’antu da faɗaɗa kasuwanci, tare da bai wa ayyukan more rayuwa muhimmanci.
A cikin rubutun nasa, shugaban ƙasar ya kawo wasu alƙaluman tattalin arziki da ya ce suna nuna ci gaban da aka samu. Ya ce, tattalin arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin 100 a ainihin darajarsa a zango na biyu na shekarar 2026. Haka kuma, ya bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya ta ragu zuwa kashi 14.63 cikin 100 a watan Satumban 2026, daga kashi 20.98 cikin 100 a daidai wannan lokaci na shekarar da ta gabata.
Ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen ajiyar ƙasashen waje na Nijeriya sun kai dala biliyan 55.1 zuwa ranar 9 ga Oktoba, 2026, ciki har da kusan dala biliyan 46 na ajiyar da aka ƙiyasta a matsayin ta ainihi bayan cire wasu nauyin kuɗaɗe. Tinubu ya ara da cewa rabon kuɗaɗen haraji da tattalin arziki ya tashi daga kashi bakwai zuwa kashi 12.5 cikin 100.
Ya danganta waɗannan sauye-sauye da matakan da gwamnatinsa ta ɗauka, waɗanda suka haɗa da cire tallafin man fetur, haɗa farashin canjin kuɗin waje zuwa tsari guda, yin garambawul ga tsarin haraji da kuma haɗa ƙarfi wajen yaƙi da hauhawar farashin kayayyaki. “Matakan da aka ɗauka tun shekarar 2023 sun kasance masu wahala, amma sun zama wajibi,” inji shugaban ƙasar.
Ya ce waɗannan matakai sun ƙara wa Nijeriya ƙarfin jawo masu zuba jari da kuma samun kuɗaɗen gudanar da ayyukan da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki na dogon lokaci. Tinubu ya kuma ce, “Amincewar masu zuba jari tana da nata farashi; kuɗin da muke biya wajen karɓar bashi yana raguwa, kuma haɗarin da ake dangantawa da zuba jari a asar ya ragu sosai.”
Shugaban ƙasar ya yi nuni da kyawawan kimantawar da hukumomin ƙasa da ƙasa masu tantance ƙimar bashi suka yi wa Nijeriya, yana mai cewa hakan alama ce ta ƙaruwa da amincewa da tattalin arzikin ƙasar. Ya ce, waɗannan kimantawa ba tallafin siyasa ba ne, sai dai sakamakon binciken hukumomin tantance ƙimar bashi na duniya, masu samar da ma’aunin kasuwanni, hukumomin sa ido da kuma masu zuba jari.
A cewarsa, kimantawar ta nuna cewa Nijeriya ta ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje, ta inganta yadda take tafiyar da tattalin arziki, sannan ta ƙara sahihanci a harkokin kuɗi. Ya ce, ingantaccen matsayin Nijeriya zai iya taimaka mata wajen jawo manyan masu zuba jari, samun rancen kuɗi na dogon lokaci da kuma rage kuɗin da take kashewa wajen karɓar bashi.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na sauya salon karɓar bashi, daga amfani da shi wajen biyan matsalolin kuɗaɗen gwamnati na ɗan gajeren lokaci zuwa zuba jari a ayyukan da za su samar da ribar tattalin arziki, guraben ayyukan yi da kuma ƙarin damammaki ga al’umma a nan gaba. Ya ce, gwamnati na kuma neman tsarin rancen kuɗi na dogon lokaci wanda zai dace da tsawon lokacin da ake sa ran kayayyakin more rayuwar da aka gina za su yi suna aiki. A cewarsa, hakan zai rage matsin lambar sake neman bashi domin biyan tsohon bashi, tare da samar da kuɗaɗen zuba jari masu rahusa.
Shugaban ƙasar ya jaddada cewa wajibi ne Nijeriya ta mayar da sabuwar amincewar da ƙasashen duniya suka nuna mata zuwa ayyukan zuba jari, kammala manyan ayyukan more rayuwa da kuma samar da fa’ida mai ɗorewa ga ’yan ƙasa.
