N70,000: NLC da TUC sun raba gari kan alawus ɗin sufuri na Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da takwararta ta ƙungiyar ma’aikatan kasuwanci da sana’a ta Nijeriya (TUC) sun raba gari kan matsayarsu game da shirin Gwamnatin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu na bayar da alawus ɗin sufuri ga ma’aikata na Naira 70,000 duk wata.

Tun da fari dai, TUC ta yi watsi da shirin Gwamnatin Tarayya na biyan ma’aikata alawus ɗin sufuri na Naira 70,000 duk wata, inda ta buƙaci a ƙara musu albashi cikin gaggawa domin rage raɗaɗin tsadar rayuwa. Shugaban TUC na ƙasa, Mista Festus Osifo, ne ya bayyana matsayar ƙungiyar a Abuja ranar Laraba, inda ya ce alawus ɗin mataki ne na wucin gadi wanda ba zai samar da sassaucin da ma’aikata ke buƙata ba.

Gwamnatin Tarayya ta amince da fara biyan alawus ɗin sufuri ga ma’aikatan gwamnati daga watan Nuwamban 2026. Ta kuma amince da biyan bashin alawus-alawus da ma’aikata ke bi, wanda za a fara biya a watan. Osifo ya ce har yanzu ba a aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a baya kan ƙarin albashi na wucin gadi ba, lamarin da ya sa ma’aikata da dama ba su samu kuɗaɗen da aka yi musu alƙawari ba. Ya tambayi dalilin da zai sa ma’aikata su amince da sabbin alƙawura alhali ba a cika waɗanda aka yi a baya ba. Ya jaddada cewa ƙarin albashi zai samar da tallafi mai ɗorewa wanda ma’aikata za su iya dogaro da shi, sabanin alawus ɗin wucin gadi.

Shugaban TUC ya kuma yi gargaɗin cewa tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi bai kamata ta zama dalilin jinkirta ƙarin albashin ma’aikata ba. Osifo ya bayyana cewa matsin tattalin arziƙi bai shafi ma’aikatan Gwamnatin Tarayya kaɗai ba, har ma da ma’aikatan jihohi da ƙananan hukumomi, ’yan fansho, ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu da masu sana’o’in hannu.

ƙungiyar ta buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai su ɗauki matakan rage farashin kayayyaki da ayyukan yau da kullum, tabbatar da biyan albashi da fansho a kan lokaci, tare da inganta yanayin aiki. Ta kuma yi kira da a samar da ayyukan yi masu inganci, bunƙasa masana’antu da sauran sassan tattalin arziƙi. Osifo ya buƙaci gwamnati ta wuce matakin sanar da manufofi, ta mayar da hankali wajen aiwatar da matakan da za su inganta rayuwar al’umma.

A nasa ɓangaren kuwa, Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) na ƙasa, Mista Joe Ajaero, ya yi tambaya kan dalilin da ya sa TUC ta ƙi amincewa da shirin Gwamnatin Tarayya na biyan ma’aikata alawus ɗin sufuri na Naira 70,000, yana mai cewa TUC ba ta cikin tattaunawar da aka yi da gwamnati. Ya ce tun daga farko NLC ta bayyana cewa tana tattaunawa da gwamnati ne da kanta, ba tare da haɗin gwiwar TUC ba, don haka ya bayyana mamakinsa kan yadda TUC ta nuna adawa da sakamakon yarjejeniyar.

Da yake magana a wata hira da aka yi da shi a shirin Morning Brief na gidan talabijin na Channels Teleɓision ranar Alhamis, Ajaero ya ce TUC ba ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba, saboda haka bai kamata ta yi adawa da tsarin da ba ta shiga tattaunawar samar da shi ba.

“Me ya sa TUC ke ƙalubalantar abin da aka samar wa ma’aikata alhali mun bayyana tun farko cewa NLC tana gudanar da wannan tattaunawa ita kaɗai?” in ji Ajaero.

Ya ƙara da cewa: “Ba TUC ce ta sanya hannu kan yarjejeniyar ba, kuma bai kamata ka yi adawa da abin da ba ka tattauna a kai ba, kuma ba ka taɓa nema ba.”

Ajaero ya ce da ya fi so TUC ta nemi alawus mafi girma domin ƙungiyoyin biyu su tattauna da gwamnati, su kuma cimma matsaya ɗaya.

“Da na fi son idan NLC ta nemi Naira ɗaya, TUC ta nemi Naira 10, watakila gwamnati ta daidaita buƙatun biyu,” inji shi.

Shugaban NLC ya bayyana cewa saɓanin ra’ayi tsakanin ƙungiyoyin ya fara ne bayan da aka ruwaito shugaban TUC yana cewa lokacin tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi zai zo ne a watan Agustan 2027.

Ajaero ya ce NLC ba ta amince da wannan matsaya ba, tana mai ganin cewa ba ta dace da doka ba. Saboda haka, ƙungiyar ta ci gaba da tattaunawa da gwamnati da kanta.

Ya ce TUC ta kuma nisanta kanta da tattaunawar bayan da wasu rahotanni suka bayyana cewa ƙungiyoyin ƙwadagon biyu suna ganawa da gwamnati tare.

“Lokacin da muka fara ganawa ta farko, kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa NLC da TUC sun yi taro. Sai suka yi barazanar ɗaukar mataki a kanmu, suka ce ba sa cikin wannan tattaunawa,” inji shi.

Ajaero ya ƙara da cewa NLC ta fitar da sanarwa domin bayyana cewa ita kaɗai ce ke gudanar da tattaunawar. “Mun fitar da sanarwa cewa NLC ce kaɗai ke cikin wannan aiki, ba tare da TUC ba. Saboda haka, zan yi mamakin dalilin da ya sa TUC za ta yi adawa da abin da aka samar wa ma’aikata,” in ji shi.

Ajaero ya ce ƙarin albashi na buƙatar bin tsari

Dangane da kiran da ake yi na ƙara wa ma’aikata albashi, Ajaero ya ce ba za a iya ƙara albashi ba tare da bin tsarin da ya dace da shigar da masu ruwa da tsaki cikin tattaunawar ba.

“Shin gwamnati tana bayar da ƙarin albashi ne a matsayin kyauta? Dole ne a samar da tsarin da za a bi,” inji shi.

Ya lura cewa TUC ce ta yi kira da a fara wannan tsari a watan Agustan 2027, yayin da NLC ta buƙaci kwamitin da ya dace ya fara aiki nan take.

Ajaero ya ce har yanzu yana nuna damuwa kan matsayin TUC game da alawus ɗin sufuri, yana tambayar dalilin da zai sa ƙungiyar ta ƙi amincewa da wani tsari da ba ta shiga tattaunawar samar da shi ba, kuma ba ita aka yi wa shi ba.

“Na daɗe ina mamakin dalilin da ya sa za ka ce ka ƙi amincewa da wani abu da ba a ba ka ba,” inji shi.

Tun da farko, jaridar PUNCH ta ruwaito cewa TUC ta yi watsi da shirin biyan alawus ɗin na Naira 70,000, inda ta buƙaci a ƙara wa ma’aikata albashi nan take.

TUC ta ce alawus ɗin albashi na wucin gadi ba zai wadatar wajen magance matsin tattalin arziƙin da ma’aikatan Nijeriya ke fuskanta ba, tana mai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da ƙarin albashi maimakon dogaro da alawus.

Shugaban TUC, Festus Osifo, da Babban Sakataren ƙungiyar, N.A. Toro, ne suka bayyana matsayar a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba.

ƙungiyar ta kuma zargi Gwamnatin Tarayya da kasa cika alkawarin biyan alawus ɗin albashi da ta yi wa wasu ma’aikata a shekarar 2023. Haka kuma, ta ce gwamnati ta yi watsi da yarjejeniyar da aka cimma watanni bakwai da suka gabata kan daidaita tsarin albashin ma’aikatan lafiya na Consolidated Health Salary Structure, ƙarƙashin ƙungiyoyin Ma’aikatan Lafiya na Haɗin Gwiwa (JOHESU).

By ukarofi

Leave a Reply