
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa INEC, ta sanar da tantance tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Dijital, Isa Ali Pantami da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a Jihar Kano, Abdulsalam Gwarzo domin shiga takara a zaɓukan 2027.
A cewar INEC, wannan nufin sai yadda sakamakon shari’o’in kotu suka kasance, waɗanda sune za su tabbatar da cancantar ‘yan takarar ko kuma akasin haka.
Saidai, hukumar ta yi watsi da ƙorafin da ɗan takarar gwamnan Jihar Ogun, Ladi Adebutu ya shigar mata, wanda ke neman ta sake nazari kan cire sunansa daga jaddawalin ‘yan takara da ta yi a baya.
Wata majiya daga INEC ta ce a zaman da aka gudanar da ranar Alhamis, hukumar ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe guda 69 daga jam’iyyun siyasa kan cire sunayen wasu ‘yan takararsu na gwamna da kujerun ‘yan majalisar dokokin jihohi.
Majiyar ta ce, guda 36 daga ciki sun yi nasara, yayin da sauran suka faɗi. Saidai ta ce hukumar tana jiran hukuncin ƙarshe daga reshenta na shari’a, wanda ke aiki kan sanarwar da za a fitar kan hukunce-hukuncen a hukumance.
Game da Pantami da Gwarzo, majiyar ta ce INEC ba ta da matsala game da takararsu saidai akwai yiwuwar hukunce-hukuncen shari’o’in kotu su shafi cancantarsu.
