
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da ware kusan Naira tiriliyan 1 domin warware matsalolin bashin ‘yan fansho a Nijeriya na tsawo shekaru 20, kamar yadda Darakta-Janar ta Hukumar Fansho ta Ƙasa (PenCom), Omolola Oloworaran ta bayyana.
Oloworaran ta faɗi haka ne a ranar Laraba a Abuja a taron satin ‘yan fansho na National Pension Week mai taken “Pension for All: Building a secure Future Together.” Da take jawabi ga tsofaffin ma’aikata da sauran masu ruwa da tsaki, Oloworaran ta ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana fifita martaba da walwalar ma’aikatan da suka yi ritaya.
Ta bayyana cewa, gwamnatin ta samar da muhimman ƙare-ƙaren kuɗin fansho a ƙarƙashin tsarin Pension Boost 1.0 tare da N32,000 ga masu karɓar kuɗaɗen fansho na sama da ƙarancin albashi. A cewarta, waɗannan gyare-gyaren suna wakiltar ƙarin mafi girma a matakin tarayya daga adadin sama da matakin mafi ƙarancin albashi.
Shugabar ta PenCom ta kuma sanar da cewa hukumar za ta ƙaddamar da shirye-shirye biyu ga walwalarsu a Nuwamba – the PennCare Health Initiative for low-income retirees da the Minimum Pension Guarantee. Ta yi bayanin cewa, Pencare zai samar da tsarin inshorar lafiya ga masu ritaya, sannan ta ce ana cigaba da gudanar da shirin pilot programme da ya ƙunshi masu ritaya 30,000.
A cewarta, “wasu mutane suna karɓar N20,000 a matsayin fansho. Wannan babban abin takaici ne da bai dace ya sake faruwa ba,” inji ta. Oloworaran ta ƙara da cewa ya kamata tsaron ritaya ya zama sama da amfanin fansho, domin bai dace ba a ce waɗanda suka yi wa ƙasa hidima na tsawon shekaru 30 zuwa 35 su ɗauki nauyin magani su kaɗai.
