Majalisar dokokin Katsina ta amince da ƙirƙirar ‘yan sandan jihohi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar dokoki ta Jihar Katsina ta amince da shawarwarin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya domin samar da damar kafa rundunar ’yan sanda ta jiha.

An cimma wannan matsaya ne bayan dukkan mambobin majalisar guda 34 sun amince da shawarwarin kwamitin musamman na majalisar, wanda shugaban masu rinjaye, Honourable Shamsuddeen Abubakar Dabai, ya jagoranta, yayin zaman musamman na majalisar.

Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Honourable Shamsuddeen Abubakar Dabai ya bayyana cewa gyaran kundin tsarin mulkin zai taimaka wajen inganta harkokin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma yi nuni da matakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, na kafa rundunar tsaro mallakar jiha, yana mai jaddada muhimmancin ƙarfafa matakan tsaro domin tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta.

Bayan amincewar majalisar, shugaban majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, ya umarci akawun majalisar da ya miƙa shawarar ga majalisar dokoki ta ƙasa domin ɗaukar matakan da suka dace.

By ukarofi

Leave a Reply