Adabi daji ne ba a yi masa ƙyaure – Khalid Imam

Spread the love

“ƙagaggen rubutu tamkar ɗa ne wajen mahaifinsa adabi”

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga: AISHA ASAS

MANHAJA: Tsakanin rubutun zube da na waƙa wanne ne ya fi wuya?

KHALID IMAM: A gaskiya tsakanin rubutun zube da na waƙa zan iya cewa kowanne ya na da irin nasa ƙalubalen ko wuya, kuma ya danganta da buƙata ko bincike ko yanayi ko irin nishaɗin da marubuci ya ke ciki a lokacin rubutawa kowanne. Wani labarin na zube ya na buƙatar dogon bincike haka ita ma waƙar. Ya na da kyau mu lura cewa ita waƙa saƙa ta ake yi kamar tabarmar kaba, shi kuma zube gina shi ake kamar yadda ake gida. Kowanne ya na da irin tasa wahalar, amma dai abin da ya ke a bayyane shi ne ba kowanne marubuci ne ya ke iya rubuta waƙa ba, duk da cewa ba duk mai rubuta waƙa ba ne ya ke da basirar ƙagar rubutaccen labari. Ni a waje na a da can waƙa ta fi ba ni wahalar rubutawa, amma a yanzu da na mayar da hankali sosai a wajen rubuta ta zan iya cewa ta fi zube sauƙi da saurin rubutawa, domin in ta zo kamar shan ruwa ta ke a waje na.

Wasu na ganin cewa marubuta a wannan zamanin suna cin karen su ba babbaka, wanda ake ganin ya haifar da yawaitar littattafai marasa ma’ana. Shin laifin waye?

Cin karen su ba babbaka kamar ya ya? Ban gane ba! In na fahimci tambayar so ki ke ki ce marubutan yanzu littattafan su ba su kai na marubutan da can inganci ba, in haka ne ai hakan ba wani mamaki domin damar da marubutan da su ka samu na yanzu ba su da ita. A lokacin su marigayi Abubakar Imam akwai kamfanoni masu yin ɗab’i kuma suna da editoci masu tace labari da gyaran duk wasu kura-kurai kafin akai ga wallafa littafi ya shiga hannun masu karatu, shin yanzu akwai irin wannan damar? Ina Maɗabi’u irin su NNPC a yau ko makamantan su? Marubuci ada rubutun kawai zai yi ya miƙa a wani lokacin ma sa shi za a yi ana kuma yi masa zagi ta hanyar nuna masa yadda zai rubuta littafin ya ƙayatar, shin yanzu marubuta su na samun irin wannan gatan? Ashe kenan daga buhu sai tukunya da ke ganin wasu marubutan su na yi ba laifin su ba ne su kaɗai, rauni ne da yadda al’amura su ka koma. Duk da cewa a yanzu ana samun cigaba marubuta su na sake fahimtar cewa aikin rubuta littafi ba na mutum shi kaɗai ba ne, akwai buƙatar editoci su duba su tace sannan akwai buƙatar sauraren shawarwari daga masana da manazarta don a haifar da littafi da zai zama zakaran gwajin dafi.

Waɗanne abubuwa ne marubucin waƙa ya kamata ya lura da su ko ya ba su muhimmanci a duk lokacin da ya ke rubuta waƙa? 

Abubuwan da marubucin waƙa ya kamata ya lura da su ko ya ba su muhimmanci a duk lokacin da ya ke rubuta waƙa a gaskiya su na da yawa sosai. Tabbas muhimmin abin lura ne mai rubuta waƙa ya tabbatar waƙar sa ta na da baitoci da ɗango da jigo (wato ta na da saƙo ko saƙonni) da ma’auni da murya da sauran su. Salon rerawa da kari da rauji muhimman abubuwan lura ne a yayin rera waƙa da dai sauran su.    

Me ya sa marubutan baya suka fi daraja a idanun mutane fiye da na yanzu?

Gaskiya sun fi mutunta al’adun Hausa a cikin rubutun su. Marubutan can shekarun suna fin daraja ne a idanun mutane masu shekaru fiye da matasan yau su ba sa ƙare basirar su wajen kwaikwayon al’adun Turawa ko Indiyawa a cikin rubutun su, ko da ma za su yi aro ne sukan baddala labarin da su ka aro ne su mayar da shi ya yi daidai da al’adu da rayuwar Hausawa. Labarurrukan da su ke cikin littafin Magana Jari Ce na marigayi Abubakar Imam babu wanda zai karanta su ya ce asalin su daga labaran Turawa ne ko na Larabawa da Turkawa saboda salon da marubucin ya bi wajen Hausantar da su. Wasu marubutan kuwa na yanzu a wajen su kwaikwayon baƙin al’adu da sunan zamani a wajen su shi ne burgewa da nuna su wai masu ilimi ne da wayewa saboda shagalta da ruɗuwa da kuma cigaban mai haƙan rijiya. Ba duka marubutan zamanin yau mutum zai karanta littattafan su ba ya ga hoton rayuwar Bahaushe sai dai akasin ta. Kai yadda ake rubuta Hausar tasirin baƙin al’adu da maƙota su kan yi naso sosai yadda za ka ji ana Hausa amma ga ta nan dai kamar ana gwaranci. Waɗannan na daga cikin wasu daga dalilan da su ka sanya darajar marubutan zamanin yau faɗuwa a idanuwan jama’a masu ilimi da masu mutunci da masu kishin Bahaushe sosai.  

Mene ne burinka a fagen rubutu?

Buruka na a fagen rubutu su na da yawa kuma mafi yawan su Alhamdulillahi Allah Ya biya mini su tun ina raye. A da can ba ni da burin da ya wuce na ga ana nazarin littattafai na a jami’o’i da kwalejojin ilimi da makarantun sakandare. Allah Ya cika mini wannan buri domin ba ma anan gida Nijeriya ba har a ƙasashen Turawa irin su Jamus da Poland da Amurika da Indiya da Nepal an yi kuma ana ci gaba da nazarin wasu daga littattafai na. A yanzu dai ba ni da burin da ya wuce na ga rubuce-rubuce na da yanzu haka na fi mayar da hankali a kan su sun zama sular ilmantar da al’umma da kuma bunƙasa musu tattalin arziki. Ina nan ina daf da fitar da wasu littattafai masu ƙoƙarin sauya tunanin al’umma akan yadda tunani ya ke da tasiri da dangantaka wajen mayar da mutum talaka ko mai arziki. Yadda talauci a yau ya ci lakar al’umma buri na shi ne waɗannan littattafai nawa su farkar da jama’a su kuma nuna wa masu karanta su hanyar zuwa ƙoramar arziki. Littafi na farko a cikin su na kira shi da sunan Zuciyar Mutum Gonarsa, wato irin tunanin da mutun ya ke shukawa a gonar zuciyarsa irin nasara ko arzikin da zai girbe a rayuwar sa. 

A matsayin ka na ɗaya daga cikin marubuta da su ka shahara, shin akwai wani shiri da ku ke yi na a gyara ko koyar da marubuta masu tasowa yadda za su inganta rubutun su?

A gaskiya a iya sani na ban san wani ƙoƙari da marubuta a ƙungiyance a yau su ke yi ba don gyara ko koyawa marubuta masu tasowa yadda za su inganta rubutun su. Ni dai a karon kaina na san ina yin ƙoƙarin koyawa matasan marubuta dabarun rubutu a wasu dandali na WhatsApp da na buɗe inda matasan marubuta su ke amfana daga tsofaffin hannu ta hanyar tattaunawa da kuma shirya musu horarwa lokaci zuwa lokaci. A cikin waɗannan dandalai akwai All Poets Network da kuma Muryar Adabi. Masana da marubuta da manazarta sukan haɗu a koyaushe a waɗannan zauruka kuma a gaskiya ana amfanar juna sosai.

Ta ya za a iya dawo da martabar rubutu?

Za a iya dawo da martabar rubutu amma fa tilas ne sai an haɗa kai, an kuma haɗa ƙarfi da ƙarfe. Hausawa na cewa hannu ɗaya ba shi ɗaukar jinka kuma tsintsiya ɗaya ba ta shara, wato sai masana da manazarta da marubuta sun haɗa kai kowa ya daina yi wa ɗan’uwan sa kallon hadarin kaji. 

Daga ƙarshe wace shawara za ka ba wa marubuta ‘yan uwan ka?

Shawarata ta ɗaya da zan ba wa marubuta ‘yan uwa na ita ce mu zama ‘yan uwa masu tuntuɓar juna da taimakon juna wajen bai wa junan mu managartan shawarwari. Shawara ta ta biyu kuma ita ce ya kamata mu daina hanzari wajen buga komai mu ka rubuta face mun bayar an tace, an tsefe kuma an gyara sosai kafin mu kai ga bugawa a matsayin littafi. Mu dinga ƙoƙarin halartar taruka na ƙara wa juna ilimi, sannan kuma mu rage haifar wa da kan mu abubuwan da za su bai wa wasu damar ganin wallen mu domin dai masu hikima na cewa sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wajen shiga. In mu ka zama tsintsiya maɗaurin ki guda za mu fi zama kusa da juna da kuma amfanar juna. A ƙarshe shawara ta ga duk marubuta musamman matasa ita ce bincike da yawaita karatu su ne manyan sirrukan da ke sa a rubuta ingantaccen littafi. Wajibi ne mu fahince cewa littafi kamar kan ɗaki ne wanda hannu ɗaya ba ya iya masa.

To madalla. Mun gode.

Ni ma na gode.

By ukarofi

Leave a Reply