Ayarin motocin kamfen na Gwamna Raɗɗa sun sha ruwan duwatsu a Malumfashi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ayarin motoci da ke kan hanyar su zuwa Funtua wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen Dikko Raɗɗa sun sha ruwan duwatsu a garin Malumfashi na Jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne a garin Malumfashi akan hanyarsu na zuwa wajan bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen 2027 a garin Funtua inda matasa ɗauke da duwatsu sukai ta farfasa gilasai na ƙanana da manyan motoci cikin su har da motar KSTA.

Haka kuma hanyar Malumfashi zuwa Mararrabar Kankara wasu matasa ɗauke da adduna sun kai hare hare a motocin APC inda suka sassari mutane da dama inda wasu mutane suka gudu suka shiga daji.

A nan filin wasa na garin Funtua inda aka gudanar da bikin yaƙin neman zaɓe, Gwamna Dikko Raɗɗa bai sami gabatar da jawabinsa saboda rashin kyakkyawar tsarin.

A ziyarar da ya kai fadar Sarkin Maska Hakimin Funtua,
Gwamnan Raɗɗa, ya bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu wajen cika alƙawuran da ta ɗauka a lokacin zaɓen 2023, inda ya bayyana cewa an aiwatar da ayyuka sama da 1,000 a faɗin yankin Funtua, ciki har da ayyuka 173 a ƙaramar hukumar Funtua kaɗai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar girmamawa da tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko ta kai fadar Sarkin Maska, Hakimin Funtua, Alhaji Idris Sambo Idris, a matsayin wani ɓangare na ayyukan buɗe kamfen ɗin zaɓen 2027 wanda yake gudana a Funtua.

Gwamna Raɗɗa ya nuna godiyarsa ga al’ummar Funtua bisa goyon baya da haɗin kai da suke bai wa gwamnatinsa, tare da jaddada irin nasarorin da aka samu a fannonin ilimi, gine-ginen hanyoyi, kiwon lafiya, samar da ruwan sha, bunƙasa noma da sauran ayyukan more rayuwa.

Ya bayyana cewa kamfen ɗin wannan karon ba zai tsaya ga yin sababbin alkawura kawai ba, sai dai zai mayar da hankali wajen gabatar da ayyukan da aka aiwatar, duba irin ci gaban da aka samu, da kuma gano ƙarin hanyoyin inganta rayuwar al’umma.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar Funtua da su ci gaba da bai wa jam’iyyar APC da dukkan ‘yan takararta goyon baya tare da yi musu addu’o’i domin samun nasara a zaɓen 2027.

A nasa jawabin, Sarkin Maska, Alhaji Idris Sambo Idris, ya nuna godiya ga Gwamna Raɗɗa bisa ayyuka, shirye-shirye da manufofin ci gaba da gwamnatinsa ta aiwatar a faɗin ƙaramar hukumar Funtua, tare da yaba wa ƙoƙarin gwamnatinsa wajen inganta rayuwar al’umma.

By ukarofi

Leave a Reply