Daga JAMIL GUlLMA a Kebbi
Waɗansu mahara da a ke sa ran lakurawa ne sun kai wani hari inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi a ƙauyukan Atuwo da Rafin Kirya da ke karamar hukumar Shanga da ke jihar Kebbi. Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkata waɗansu.
Wani ɗan asalin garin na Atuwo Malam Idris Lawal ya bayyana cewa maharan sun zo ne a kan babura inda suka budewa mutanen garin wuta wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama bayan sun bar garin kuma suka wuce garin Rafin Kirya a can ma suka buɗe wuta kafin su ƙara gaba.
Ya bayyana cewa ba zai iya tantance adadin mutanen da suka rasu ba amma dai suna da yawa.
Ya yi kira ga hukuma da ta taimaka ta girke jami’an tsaro saboda su sami damar ɗibar amfanin gona da suka samu. Ya bayyana cewa jim kaɗan bayan harin, ɗan takarar majalisar wakilai na ƙananan hukumomin Yauri, Shanga da Ngaski Honarabul Yusuf Tanko Sununu ya aika da wakilai a waɗannan ƙauyukan domin jajenta musu tare da ba su tallafin kuɗi da na abinci.
