Daga IBRAHIM HAMISU
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya ayyana jihar a matsayin “jihar Asiwaju”, yayin da yake bayyana goyon bayansa ga shugaban ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Fintiri ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da gangamin ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement, inda aka kuma ƙaddamar da motocin da za a bai wa masu gudanar da ayyukan ƙungiyar a jihohi 14 domin ƙarfafa ayyukan wayar da kan jama’a da tuntuɓar al’umma gabanin zaɓen 2027.
An ce motocin za su taimaka wajen gudanar da ayyukan yaɗa manufofin ƙungiyar da kai saƙon kamfen zuwa ƙananan hukumomi da al’ummomi daban-daban, yayin da ƙungiyar ke faɗaɗa ayyukanta a faɗin ƙasar.
Da yake jawabi a wajen bikin miƙa motocin, mai gudanar da ƙungiyar na ƙasa, Sunday Adekanbi Asuku, ya buƙaci waɗanda suka amfana da motocin da su ƙara haɗin kai tare da ƙarfafa hulɗa da jama’a a matakin ƙasa.
Asuku ya kuma yi kira ga masu gudanar da ayyukan ƙungiyar a jihohi da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da neman goyon baya ga ƙoƙarin sake zaɓen Shugaba Tinubu.
A cewar ƙungiyar, samar da motocin na daga cikin matakan da take ɗauka domin tallafa wa masu gudanar da ayyukanta wajen isa ga al’ummomi da kuma isar da bayanai kan ayyukan gwamnatin Tinubu da manufofin ajandar “Sabuwar Fata”.
Ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da faɗaɗa ayyukanta zuwa wasu jihohi ta hanyar gudanar da shawarwari da ƙara tuntuɓar al’umma.
Shirin wayar da kan jama’a na ƙungiyar ya ta’allaka ne kan tuntuɓar ‘yan Nijeriya kai tsaye, inda masu gudanar da ayyukan ƙungiyar a jihohi da ƙananan hukumomi za su jagoranci ayyukan kamfen na kai saƙo gida-gida.
