Dalibai 108 masu ƙarancin shekaru kacal suka tsallake shiga jami’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Ilimi na Tarayyar Nijeriya, Tunji Alausa, ya bayyana cewa ɗalibai 108 kacal cikin kusan 39,000 da suka yi jarrabawar UTME ta shekarar 2026, suka yi nasarar tsallake tantancewar Gwamnatin Tarayya domin samun damar shiga manyan makarantu tun kafin su kai shekara 16.

Alausa ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja, lokacin da yake karɓar ɗalibai biyu da suka fi kowa maki a jarrabawar UTME ta bana, tare da wasu matasa shida da suka yi fice duk da kasancewarsu ƙasa da shekarun da aka ƙayyade domin shiga jami’a. Magatakardar Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta ƙasa (JAMB), Segun Aina, ne ya gabatar da ɗaliban ga ministan.

Ministan ya ce, ɗaliban da suka yi nasarar tsallake tantancewar sun nuna ƙwarewa ta musamman a fannin karatu, tare da tabbatar da cewa suna da cikakkiyar fahimta, natsuwar zuciya da zurfin tunani da ake buƙata domin fuskantar ƙalubalen karatun jami’a. Ya bayyana cewa, an tsara tantancewar ne ta matakai daban-daban, domin tabbatar da cewa baiwar da wasu yara ke da ita ba za ta sa a shigar da su manyan makarantu kafin su kasance a shirye ba. A cewarsa, ɗalibai 2,244,149 ne suka yi rajistar jarrabawar UTME ta shekarar 2026, yayin da 2,174,396 suka zauna domin rubuta jarrabawar.

Daga cikin waɗanda suka rubuta jarrabawar, kusan 39,000 ba su kai mafi ƙarancin shekarun shiga manyan makarantu da aka ƙayyade, wato shekara 16, ba. Alausa ya ce daga cikin waɗannan matasa, 391 ne kawai suka samu maki 320 ko sama da haka. Sai dai bayan gudanar da ƙarin tantancewa, adadin waɗanda suka cancanci a yi la’akari da shigar da su manyan makarantu ya ragu zuwa 108.

Ya bayyana waɗannan ɗalibai a matsayin masu baiwa ta musamman, yana mai cewa adadinsu ya kai kusan kashi 0.005 cikin ɗari na dukkan waɗanda suka rubuta jarrabawar. “Ku ne haziƙan da suka yi fice a cikin al’ummarmu,” inji ministan yayin da yake jawabi ga ɗaliban. Ya ƙara da cewa, “Ku ne za ku kawo sauyi a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙirenku.”

Ministan ya ce, wajibi ne gwamnati ta gano yara masu baiwa ta musamman, ta tallafa musu tare da raya hazakarsu, domin su zama ƙwararrun masu ƙirƙira waɗanda za su samar da hanyoyin magance matsalolin da Nijeriya da sauran ƙasashen duniya ke fuskanta.

Alausa ya jaddada cewa ƙayyade mafi ƙarancin shekarun shiga manyan makarantu zuwa shekara 16 ba yana nufin gwamnati na son hana yara masu hazaƙa damar ci gaba da karatu da wuri ba ne. A maimakon haka, manufar ita ce tabbatar da cewa matasan sun kai matsayin balagar da za ta ba su damar fuskantar rayuwar jami’a.

Ya ce, ƙwarewa a fannin karatu kaɗai ba ta isa ta tabbatar da cewa ɗalibi ya cancanci shiga jami’a ba, domin karatun manyan makarantu na buƙatar natsuwar zuciya, zurfin tunani da kuma iya fuskantar ƙalubalen zamantakewa da na karatu. Ministan ya buƙaci ɗaliban da suka yi nasara su ɗauki baiwar da Allah ya ba su a matsayin nauyin da ke kansu na taimaka wa al’umma, ba wai kawai wata dama ce ta shiga jami’a da wuri ko samun ci gaba na kansu ba.

Da yake danganta hazaƙar matasan da makomar ci gaban ƙasa, Alausa ya ce yawan matasa da Nijeriya ke da su wata babbar dama ce da ya kamata a yi amfani da ita ta hanyar inganta iliminsu da bai wa ƙwarewarsu damar bunƙasa.

Ya ƙiyasta yawan al’ummar Nijeriya da kusan miliyan 220, inda matsakaicin shekarun jama’a ya kai shekara 18.5. Ya ƙara da cewa kusan kashi 70 cikin ɗari na al’ummar ƙasar ba su kai shekara 30 ba.

A cewarsa, sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa a fannin ilimi na da nufin faɗaɗa damar samun ilimi ga matasan Nijeriya, tare da ƙarfafa ƙasar wajen mayar da hazaƙarsu zuwa ƙirƙire-ƙirƙire da hanyoyin magance matsalolin al’umma. Alausa ya taya ɗaliban murna a madadin Shugaban ƙasa Bola Tinubu da Ma’aikatar Ilimi, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa hazakarsu za ta iya haifar da sabbin nasarori da za su amfani miliyoyin mutane.

A wajen taron, ministan ya bai wa ɗalibai takwas da aka karrama, ciki har da waɗanda suka fi kowa maki a jarrabawar UTME ta bana, lambobin yabo da takardun shaidar karramawa. Daniella Owoeye ce ta zo ta farko da maki 372, yayin da Enwere Kingsley Ikenna ya zo na biyu da maki 370.

By ukarofi

Leave a Reply