Kotu ta umarci El-Rufa’i ya fara kare kansa a shari’ar naɗar hirar Ribaɗu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i da ya fara yunƙurin kare kansa idan ya so hakan a shari’ar da ke zargin sa da naɗar hirar wayar tarho ba bisa ƙa’ida ba ta Mai ba wa Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu.

Alƙalin ta bayar da wannan izini ne yayin da take gudanar da hukunci kan ƙorafin El-Rufa’i na bayar da amsa kan zargin, inda ya nemi da ya ƙalubalanci ƙarar zargin da aka shigar akansa game da iƙirarin.

Mai Shari’ar ta kuma yi watsi da ƙorafin El-Rufa’in ta amsa ga wadda masu ƙara suka gabatar, inda ya ce sun gabatar da wadatattun hujjoji da suka bayar da damar tsohon gwamnan ya nemi kare kansa idan ya buƙaci hakan.

Wannan hukunci na nufin, an ba wa El-Rufa’i damar ji ta ɓangarensa akan zarge-zargen da ake masa yayin cigaba da shari’ar.

Sauran bayani zai biyo baya…

By Babaji

Leave a Reply