Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da cigaban al’umma (CITAD) ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ƙara zuba jari wajen samar da ƙirƙirarriyar fasaha wato (AI) a cikin gida, tare da ƙarfafa ikon Nijeriya na sarrafa bayananta, domin rage dogaro da fasahohin ƙasashen waje.
Babban daraktan cibiyar, Malam Yunusa Zakari Ya’u, ne ya yi wannan kira a cikin jawabin maraba da ya gabatar a taron Kano Social Influencers Summit (KANSIS) karo na bakwai na shekarar 2026, wanda aka gudanar a Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu (KHAIRUN), Kano, a ranakun Laraba da Alhamis. Wanda Malam Isa Garba ne ya wakilce shi a wajen taron.
Ya’u ya ce Nijeriya na buƙatar wuce matakin sayen kayayyaki da ayyukan AI daga ƙasashen waje, ta koma ƙirƙira da mallakar fasahar da kanta, domin bunƙasa ƙere-ƙere da samar da hanyoyin magance matsalolin shugabanci.
Ya ce matasan Najeriya na da basira da ƙwarewar da za su iya amfani da su wajen samar da sabbin fasahohi, sai dai suna buƙatar yanayin da zai ba su damar mayar da tunaninsu da ƙirƙirarsu zuwa ayyukan da za su amfani al’umma. Ya buƙaci gwamnati ta tallafa wa matasa masu ƙirƙira tare da samar da damar bunƙasa fasahar AI ta cikin gida.
Ya’u ya kuma nuna damuwa kan yadda ake sarrafa bayanai a Najeriya, yana mai cewa yawancin bayanan ƙasar na cikin tsofaffin tsare-tsaren adana bayanai da ba su da cikakkiyar haɗin kai, lamarin da zai iya kawo cikas ga ƙoƙarin ƙasar na ƙirƙira da mallakar fasaharta.
Ya yi kira da a ƙarfafa dokoki da tsare-tsaren kula da bayanai, tare da tabbatar da cewa kamfanonin fasaha na ƙasashen waje suna ɗaukar alhakin yadda suke tattarawa da amfani da bayanan ’yan Najeriya da cibiyoyinsu.
Ya ce, “Dole ne mu riƙa ɗora wa kamfanonin ƙasashen waje alhakin duk bayanan da suke tattarawa daga ’yan ƙasarmu da cibiyoyinmu.”
Daraktan ya ƙara jaddada muhimmancin samar da wutar lantarki da ruwan sha cikin aminci da araha, yana mai cewa waɗannan muhimman abubuwa ne wajen tafiyar da cibiyoyin adana bayanai da bunƙasa fasahar AI. Ya yi gargaɗin cewa gina cibiyoyin adana bayanai kaɗai ba zai tabbatar da samun ’yancin fasaha ba idan ba a magance matsalolin muhimman ababen more rayuwa ba.
Ya ce, “AI ba za ta maye gurbin ayyukan more rayuwa na yau da kullum ba, kamar samar da wutar lantarki da ruwa a kai a kai cikin farashi mai sauƙi.” Ya ƙara da cewa wajibi ne a tabbatar ana tattarawa da adana bayanan ƙasa tare da amfani da su cikin gaskiya da bin dokokin da suka dace.
Taken taron na bana shi ne “Makomar Shugabanci: Ƙirƙirarriyar Fasaha (AI), Ƙirƙire-Ƙirƙire da Shigar ’Yan Ƙasa Cikin Harkokin Gwamnati.” Taron ya haɗa masana da masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda sabbin fasahohi za su iya inganta shugabanci, ayyukan gwamnati da sa hannun jama’a wajen yanke shawara.
Ɗaya daga cikin masu gabatar da takardu a taron, Dakta Usman Bugaje, ya ce ƙirkirarriyar fasaha (AI) na iya taimaka wa jami’an tsaro wajen gano masu aikata laifuka da bin diddigin su.
Mataimakin shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Haruna Musa, na daga cikin waɗanda suka halarci taron, tare da Farfesoshi Jibrin Haruna, Auwal Musa Rafsanjani, Isa Sanusi da Farfesa Abdallah Uba Adamu, da sauran mahalarta.
Tun bayan fara shi a shekarar 2019, taron KANSIS ya zama dandalin tattaunawa kan fasahar zamani, shugabanci, adalci da shigar jama’a cikin harkokin al’umma.
