12
Mar
DAGA MUKHTAR YAKUBU Idan ana magana a game da marubuta da suka bayar da gudunmawa a ƙasar Hausa musamman ta fuskar matasa, to Malam Kabiru Musa Jammaje yana cikin sahun gaba. Duk da kasancewar sa marubucin harshen Turanci ne shi, amma gudunmawar da ya bayar ta zarta ta wasu marubutan Harshen Hausa ne ba kusa ba. Domin kuwa kasancewar sa malami a harshen Turanci, ta sa ya rinƙa buga littattafai domin koyon harshen Turanci a tsakanin matasan mu, wanda hakan ya sa matasa da dama suka koyi yaren Turanci cikin sauƙi kuma har suka zama abin alfahari a gare mu.…