Ya kamata marubuta su riƙa taimakawa mabuƙata – Nimcyluv

“Na ciyar da mabuƙata fiye da ɗari cikin Ramadan”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Tun da watan Ramadan ya kama a wannan shekara, marubutan adabi maza da mata suka shiga cikin hidimar kyautata addininsu da kusancinsu da Allah, ban da shirye-shirye da suke gabatarwa a zaurukansu na Facebook da whatsapp, wasu kuwa har ƙungiyoyi ne da su da suke tallafa wa mabuƙata da ciyar da su abincin buɗe-baki. Na’ima Suleiman Sarauta na daga cikin marubutan da suke gudanar da irin wannan aikin neman lada na ciyarwa da taimakon marayu. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Nimcyluv kamar yadda aka fi saninta ta bayyana masa fatan ta na ganin marubuta adabin Hausa sun kafa wata gidauniya na tallafa wa junansu da sauran mabuƙata. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanki.

NIMCYLUV: Sunana Na’ima Sulaiman Shu’aibu, amma an fi sanina da Na’ima Sulaiman Sarauta, ko kuma Nimcyluv, musamman a zaurukan sada zumunta.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarki.

Ni ƴar asalin Jihar Kano ce daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso. An binne cibiyata a Unguwar Sheka a Gidan Dagaci. Na yi karatuna na Islamiyya a makarantar Zaidu Bin Thabit wacce kuma a nan na yi saukar Alkur’ani mai girma. Na yi makarantar firamare a Nagarta Standard Academy, wacce take nan Sheka, na kuma yi karatun sakandire a makarantar Talk Quality College a shekara ta 2015. Na fara karatun jami’a a ɓangaren koyon aikin jarida a Jami’ar Bayero da ke Kano, amma zangon farko karatun nawa ya tsaya sakamakon jinya da na yi mai tsayi wacce ta dawo da karatuna baya. Sai dai a cikin ikon Allah yanzu ina shirye-shiryen komawa makaranta. Kodayake ina son sauya sheƙa idan Allah Ya nufa ko kuma na haɗa duka biyun wajen karantar aikin jarida da nazarin Harshen Hausa, saboda inganta rubutun adabi da nake yi.

Ina aiki da wata ƙungiya mai zaman kanta ta NGO. Sannan ina kuma gudanar da kasuwancina a ɓangaren rubutun littattafan hikaya da nake yi. Ni ce kuma shugabar ƙungiyar Mikiya Writers Association wacce muke da marubuta wajen 55 a cikinta, inda muke taimaka musu a ɓangaren cigaban rubutunsu. Haka kuma ina riƙe muƙamin mai kula da walwalar ƴan ƙungiya wato Welfare a Ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Kano ta GAMJIK. Yanzu kuma haka ina shirye-shiryen yi wa ƙungiyata mai suna SARAUTA CHARITY FOUNDATION rijista.

Littattafai nawa ki ka rubuta, kuma wanne ne ki ka fi samun alheri da shi?

Na rubuta littafai a ƙalla sama da goma sha biyar, kuma cikin yardar Allah na samu alheri a kowanne. Duba da cewa kullum ana tafiya tunani na ƙara kaifafa, kuma muna zurfafa bincike wajen ganin abinda zai ja hankalin masu karatu wanda hakan ke sa wa kowanne labari ya karvu kuma ya yi yawo a duniyar yanar gizo (trending). Sai dai na fi samun alheri a littafin ‘Mijin Malama’ da kuma ‘Munafukin Miji’.

Daga cikin littattafan da na rubuta akwai, ‘Moon’, ‘Uncle Ne’, ‘Tsintacciya’, ‘Zain-Abeed’,
‘Abu-Maleek’, ‘Dare da Duhu’, ‘Jidda’, ‘Juyayi’, ‘Auren Fansa’, ‘Izzar So’, da kuma ‘Sabon Sarki’.
Yanzu kuma ina kan aikin wasu uku. ‘Ɗan Malam’, ‘Diyaana’, sai ‘Budurwar Daji’.

Wanne sauyi za ki iya cewa kin samu a rayuwarki ta dalilin rubutu?

Daga fara rubutuna zuwa yanzu ban san wanne sauyi zan ce na samu ba, amma ina da yaƙinin na samu cigaba sosai, kuma ina dab da cimma nasara a kan burina na rubutu. Na samu sauyi a yanayin mu’malata da mutane, na samu sauyi a gida, a waje, da kuma ta kafafen sadarwa na zamani.

Yaya ki ke samun hikimar yin rubutu da samun jigon da ya dace ki yi rubutu a kai?

Jigo shi ne labari gabaɗaya, labari kuma shi ne abinda jigo ya bayar da shi. Kafin samun jigon da zan yi rubutu a kai ina kallon duniya ne bakiɗaya, kuma ina juyata daga yadda mutane ke ganinta zuwa inda ni zan kalleta da idanun zuciya. Kuskure nake fara hangowa na al’ummarmu kafin na gano abinda yake daidai, idan an ce mace na kashe miji akan auren dole sai na juya shi zuwa miji ya kashe matarsa, bi ma’ana na farfaxo da mutane daga abinda suka yi makuwa a kai, tunda ai da mace da namiji duka zuciya ce da su. Za ta iya ayyanawa kowa abu mai kyau da akasin hakan. Ina samun jigon da mutane da yawa suke ganin abin ba zai faru a zahiri ba, sai kuma sun ji labarin sai su gasgata fandisho na ginin.

Abu na biyu kuma ina kallon mutanen da suke kusa da shi su waye su? Me suke yi? Yaya suke gudanar da rayuwarsu musamman ta aure? A wannan ɓangaren ma ina fitar da jigo. A ɓangaren soshiyal midiya ma ina baza idanu, domin shiruna ya fi maganata yawa, bincikena ya fi aikina yawa. Yanayi ke sawa a fitar da jigon labari.

Wanne lokaci ki ka fi jin daɗin yin rubutu?

Na fi jin daɗin yin rubutu cikin dare, yayin da gari ya yi shiru ba surutu ba hayaniya. Hakan yana mini daɗi, ina rubuta abinda nake so har ma wanda ban yi tsammani ba.

Yaya ki ke haɗa aikin rubutu da sauran ayyukan da ki ke gudanarwa na rayuwa?

Wannan abu ne mai sauƙi duk da an ce ba a haɗa gudu da susar ɗuwawu, ko kuma taura biyu a baki bata taunuwa. Amma idan har mutum ya tsara yadda zai dinga gudanar da abubuwan shi wannan mai sauqi ne. Idan na farka ina sanin me zan yi har zuwa kwanciyar barci duk abinda babu shi a jadawalin da na yi na wunin bana yin shi, kamar yadda ba na rubutu a ranakun Asabar da Lahadi. Haka kuma kamar yadda na tsara a yanzu a shekara littafi xaya zan riƙa yi ko biyu.

Kin ce kina aiki da ƙungiyoyi masu zaman kansu na taimakon al’umma, waɗanne ayyuka ku ke gudanarwa?

Muna taimakawa marayu da kuma nakasassu, sai kuma yaran da ba sa zuwa makaranta da waɗanda iyayensu basu da ƙarfin ɗaukar nauyin karatun su.

Akwai wasu marubuta da suka kafa gidauniya don neman tallafi ga wasu mutane da ke fuskantar ƙalubalen rayuwa, menene ra’ayinki game da taimakon da suke bayarwa?

Wannan abu ne mai kyau domin akwai mutanen da suke buqatar taimako sosai. Misali, idan ni ina da gidauniya kuma a iya Kano take aiki, sai wata ta buɗe wata gidauniyar ita kuma ta Kaduna ko Neja, ka ga hakan ya taimaka. Sannan duk ƙoƙarin wata gidauniyar ba lallai ta hango wasu wanda ya kamata a ce hankali da idanun mutane sun kai kan su ba. An ce hannu da yawa maganin ƙazamar miya, kuma hannu ɗaya baya ɗaukar jinka. Yawan masu gidauniyar zai taimaka wajen rage matsalolin mabuƙata.

Wanne abu ne ya ƙarfafa miki gwiwa ki ka ga ya dace ke ma ki kafa taki gidauniyar?

Zuciyata! Duk abinda zuciya ta yanke mini ina jin kawai zan iya; ban yarda da karaya ko kasawa ba, ballantana faɗuwa. A mahanga ta zahiri tun a aikin NGO na ji ina son buɗe gidauniyar taimakawa mutane. Sannan a wani ɓangaren kuma iyayena su ne ƙarfin gwiwata, kullum suna ce mini zan iya idan na yarda da hakan. Sai kuma madubina Fauziyya D. Sulaiman, wacce koyaushe na kalleta sai na ji na qara samun wani ƙwarin gwiwa kan abin da zuciyata ta yarda da shi.

Waɗanne ayyukan jinƙai ku ke gudanarwa, kuma a ina ku ke samun tallafi?

Muna samun tallafi ne daga wajen mutane sannan mu na yi da aljihunmu, duba da cewa gidauniyar ba ta gama zama sananniya ba. Wasu kuma suna shakkar bada tallafi da tunanin ko ba za mu bayar ba. Kamar yadda na faɗa a baya, duk wanda ya zo da buƙata na neman taimako muna yin iya bakin ƙoƙarinmu wajen ganin an yi masa, muna bincika wa unguwa wajen nemo yaran da basa zuwa makaranta ko makafi da guragu. Fatanmu jama’a su saka hannu a wannan gidauniya ta Sarauta Charity Foundation su bamu nasu tallafin ta hanyar taimaka mana da kuma yaɗa manufarmu.

Duk shekara marubuta adabi na amfani da watan Ramadan wajen gudanar da wasu abubuwa na gyaran imani da qara kusantar ubangiji, ke waɗanne abubuwa ki ke yi a matsayinki ta marubuciya da kuma a ƙungiyance, a wannan lokaci?

Watan Ramadan wata ne da babu kamar shi a jerin watannin Musulunci. Ko baka tava yin wani abu ba yana da kyau ka yi a lokacin. Muna ciyarwa a watan Ramadan tun daga farkon watan har ƙarshe. A ƙungiyance kuma muna dakatar da rubutu har sai zuwa bayan sallah domin mu ribaci watan ta hanyar sauke karatun Alƙur’ani, da kuma shirya wasu shirye-shirye na addini domin magoya bayanmu, wato masu bibiyar littattafanmu, tare da gabatar da Gasar Kacici-Kacici har da wata kyauta ta musamman ga waɗanda suka fi samun nasara, a shirin ‘Gamu Ga Ramadan’.

Mun ga kina sanya irin ayyukan rabon abincin buɗe-baki ga mabuƙata a shafukanki na sada zumunta, a ina ki ka samu kwangilar yin wannan aiki?

Ba kwangila ba ce, aikin alheri ne, na taimakawa. Tun farko ina yi ne daga aljihuna, na daga abinda Ubangiji ya bani, ganin ayyukanmu ya sa wasu mutane suke bamu tallafin kudi ko na danyen kayan abinci. Kamar wannan watan mun samu tallafi da yawa har daga Gidauniyar Aliko Ɗangote. Mun samu abincin mutane guda ɗari. Babu wanda ke ba mu kwangila, muna yi ne ƙarƙashin gidauniyar Sarauta Charity Foundation.

Kawo yanzu mutane nawa ne suka ci moriyar wannan shirin sadakar abincin buɗe-baki da ku ke bayarwa?

Gaskiya ba zan iya sanin adadin mutane nawa muka ciyar ba kawo yanzu. Amma na san mun je makarantun allo, inda muka rabawa almajirai da yawa abinci. Mun kuma je gidan gyaran hali, nan ma mun bayar da gudunmawar abinci. Sannan da jama’a cikin gari. Kullum muna dafa abinci muna bayarwa sadaka ga mabuƙata.

A cikin marubuta akwai wasu da ki ka sani masu gudanar da irin wannan aiki da ku ke yi?

E, akwai su. Na san akwai Fauziyya D. Sulaiman, akwai kuma Bilkisu Musa Galadanci, da Zuwairiyya Adamu Gerei, duk suna da ƙungiyoyi da suke ciyarwa da kuma tallafawa mabuƙata.

Menene za ki ce ga marubuta maza da mata da ke amfani da watan Ramadan wajen vullo da ayyukan jinƙai na taimakon al’umma?

Allah ya saka musu da mafificin alheri, kada su ga ji su ci gaba ladan su yana a rana gobe ƙiyama duk wanda ya taimaka wajen faranta ran wani Ubangiji zai faranta nasa.

Kina ganin menene hikimar da ke sa wasu marubuta jingine yin rubutu a cikin watan Ramadan?

Hikimomi ne da yawa. Na farko domin samun cikakken lokaci na yin ibada da kula da iyalai. Da kuma tsayar da zuciyar masu karatun zuwa ga ibada duk bamu da tabbaci akan makomarmu na yin wannan rubutun. Dole mu nutsu mu roƙi Allah yafiya da kuma dacewa, kuma mu samu damar yin ibada cikin nutsuwa. Sai dai hakan ba ya nufin ba a yin bincike ko tunani, domin shi rubutu ciwo ne a zuciya!

Kina ganin akwai wani abu da marubuta za su ɓullo da shi a irin wannan lokaci, wanda al’umma za ta amfana da gudunmawarsu?

Yadda ake haɗuwa a tatauna akan rubutu yana da matuƙar muhimmanci. Haka kuma yadda ake samun ƙungiyoyin marubuta a ce akwai wata ƙungiya ta marubuta daban wacce a ciki za a iya samun shugabannin kowacce ƙungiya ta marubuta wajen ganin an taimaki mabuƙata ko kuma a saka jagororin kowacce jiha a gina ƙungiya guda ta marubuta, wacce za a riqa taimakon al’umma kawai.

Akwai wasu marubuta da ke taimaka miki wajen tafiyar da wannan aiki na taimakon mabuƙata da ku ke yi?

Babu wasu marubuta da suke taimaka mini wajen gudanar da aikin nan. Ni nake kiɗana da rawata.

Menene saƙonki ga marubuta albarkacin wannan wata mai alfarma?

Duk wanda aka cewa marubuci ana da tabbacin za a samu nutsuwa, hankali, kamewa, sanin ya kamata a tattare da shi. Mu yi amfani da tunaninmu, da fikirarmu wajen ganin mun kawo abu sabo wanda zai taimaki mutane cikin watan Ramadan ko kuma mu saka hannu wajen taimakawa marubuci ko marubuciyar da ke gudanar da wani abu na jinƙan al’umma.

Na gode.

Ni ce da godiya.