Matan aure barka da Ramadan! (3)

Tare da AMINA YUSUF ALI

Masu karatu barkanmu da sake kasancewa a wani makon a filinku mai albarka a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako mun zo muku da ci gaba na maudu’in nan mai taken matan aure barka ramadan. Allah ya kawo kashi na uku kuma kashin ƙarshen wannan maudu’in da muke kawo muku girke-girke kala-kala wand amarya ko Uwargida za su samu su sabunta tukwanensu ga mai gida da sauran iyali saboda zuwan watan Ramadan mai albarka su ma su samu su samu ƙarin lada da rahamar Ubangiji Subhanahu wata’ala. Kamar yadda kuka sani da ma wannan fili ya yi fice wajen kawo hanyoyin gyara varakar aure da inganta zamntakewar aure. To har a cikin wata mai alfarma ma ba a bar mu a baya ba. Allah ya amshi ibadunmu da addu’o’inmu na wannan wata mai alfarma da yake shirin bankwana da mu. Allah ya sa mu ga ƙarshensa cikin ƙoshin lafiya.

Ga wasu girke da muke kawo muku a wannan mako:

  1. Yadda ke donot (doughnuts)

Abubuwan haɗawa:
Fulawa kofi 3
Bota rabi
Kwai 3
Mangyaɗa
Suga rabin kofi
Gishiri rabin cokali
Yis (yeast) cokali xaya
Baƙar hoda cokali 1 (idan kana buƙata. Amma za a iyabyi ko ba ita).

Yadda ake haɗawa:

Da farko za ki tankaɗe fulawarki a kwano mai faɗi.

Sai ki sa yis da baqar hoda ki juya, sai ki sa bota ki yi ta juyawa ya haɗu da fulawan sosai.

Sai ki fasa ƙwanki ki zuba ki juya ya haɗu da fulawar.

Sannan sai ki zuba suganki a ruwan ɗumi ki juya sai ki zuba a fulawar ki kwava da ɗan gishiri. Kada ya kai kaurin cin-cin kuma kada ya yi ruwa kamar fanke.

Idan ya yi sai ki duddunƙula su ki mulmula ki jera a farantai ko a buhu mai faɗi. Sai ki sa a rana ya yi kamar minti arba’in.

Sai ki duba idan ya tashi sai ki ɗora kaskonki a wuta ki sa mangyaɗa. Sai ki dinga ɗauka ɗaya bayan ɗaya kina musu ƙofa a tsakiya kina jefawa a man nan mai zafi.

Ko kuma ba sai kun dunƙula shi ba kawai ki bar kwaɓin a haka, idan ya tashi sai kuma ki kawo gwangwanin madara na ruwa don ki samu ya yi rawun sai ki sa a paranti ki dinga murzawa kina sa wannan gwangwanin kina fitar da rawun din donut dinki, kuma ki na sa wa a mai kina soyawa, hakan za ki yi ta yi har ki gama.

shi donot idan ya tashi sosai za ki ga cikinsa ya yi fanko haka. To za ki iya ɗura wani abu ko madara ko cakuleti a ciki don ƙara masa armashi. Irin wannnan shi ake kira da ‘fillings’ a turance.

Ga yadda ake haxa madarar sa wa a donot.

Suga kofi ɗaya
Bota jaka ɗaya
Madarar gari jaka uku
Condensed Milk (majinar bature) kofi uku.
Filebo na Vanilla extract cokali 1
A zuba bota a cikin babbar roba sai a yi ta bugawa, har sai ta yi fari sosai.
Daga nan a zuba suga a zuba a kai tare da madara a juya sosai har sai ya yi kamar ‘cream’ sannan a sa a zuba ‘condensed milk’ (majinar bature) da vanilla a ƙara juyawa.

Shikenan madara ta kammala sai ki naɗa kwarkwaro ki yi wa donot qofa daga gefensa ki yi ta ɗurawa.

Idan kina son ki yi mai cakuleti za ki sa masa garin cakuleti a matsayin garin madarar da kika sa a haɗin sama. Amma idan garin cocoa kika sa dole ne sai kin sa madara. Haka kuma za ki iya amfani da cakuletin Nutella, Idan da hali.

2 Yadda ake lemon citta

Abubuwan da ake buqata
Ɗanyar citta
Kanumfari
Lemon tsami
Sukari
Filebo
Kalar lemo

Yadda ake haɗa lemon citta

Da farko za ki samu citta ki kankare ta ki yankata kanana sai ki sa kanumufari ki markaɗa su, sai ki tace ki sa sukari, da lemon tsami bayan kin matse shi kin tace. Sannan ki sa filebo da kuma kalar lemo da garin lemo (tiara ko jolly) in kina buqata sai ki sa a firji ya yi sanyi shikenan.

  1. Yadda ake sinasir

Kayan haɗi:
Farar shinkafa ta tuwo
Baƙar hoda
Suga
Yis (yeast)
Gishiri
Yadda zaki haɗa

Da farko uwargida ko amarya za ki wanke shinkafarki, ki rege idan akwai tsakuwa, sai ki dafa wata daban ki haɗa a kan ɗanyar ki bayar a markaɗo miki, sai ki sa yis da suga da baƙar hoda, za ki iya sa gishiri kaɗan sai ki juya kamar dai yadda ake kwaɓin wainar shinkafa amma kwavin sinasir yafi na wainar shinkafa ruwa. Daga ban sai ki sa kwavin a rana in ya tashi sai ki dauko kaskon suya mara kamu (non-stick) ki soya mangyada da albasa saboda wani man yana da wari, in kika soya sai ki juye a kwano, sai kuma ki samu auduga mai kyau ko ’tissue’ burushin girki, sai ki dinga dangwalo man da shi kina shafawa a kaskon. Daga nan sai ki zuba ƙullinki ki rufe ki bar shi zuwa ‘yan mintuna, sai ki cire ba a juya sinasir. Hakan za ki yi ta yi har ki gama. Sai a yi miya mai kyau aci da ita. Ana cin sinasir da miyar ganye, ko miyar taushe ko agushi da makamantansu.

To a nan muka kawo ƙarshen wannan maudu’in mai taken matan aure barka da Ramadan! Allah ya ba mu ladan abinda muka yi dai-dai, Allah ya ba mu lada. Na kuskure Allah ya yafe mana.

A nan nake cewa, masu karatu a yi sallah lafiya.