Gwamna Zulum ya samu nasarorin bunƙasa rayuwar al’ummarsa – Hon. Ayuba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Borno, Hon. Bello Ayuba ya lissafo wasu nasarorin da mai girma gwamnan jihar Farfesa Baba Gana Umara Zulum ya samu, inda ya bayyana gwamnan a matsayin mutum mai kishin al’umma da jiharsa.

Hon Bello Ayuba ya ce Gwamna Babagana Umara Zulum ya samu ɗumbin nasarori musamman  a fannin inganta rayuwar bil’adama da sauransu.

Shugaban Jam’iyyar APCn ya ce Gwamna Zulum ya bunƙasa ababen more rayuwa da shirye-shiryen da suka shafi jama’a kaitsaye kamar gina gidaje, gina manyan tituna a cikin gari da ƙauyaku a ƙananan hukumomi 27 da gina gadar sama a Maiduguri, babban birnin jihar.

Kazalika ya ce Zulum ya yi ƙoƙari wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya ta fuskar sayo kayan taimakawa tsaro ga jami’an tsaro da hukumar tsaro ta CJTF don yaƙi da ƙungiyar Boko Haram.

“Samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya a ƙananan hukumomi 27 da inganta wasu cibiyoyin lafiya a wasu ƙananan hukumomi da gundumomi a jihar Borno.

“Haka kuma Maigirma Gwamna ya samar da ayyukan yi ga matasa da horar da matasa kwasa-kwasai a fannin ilimin likitanci da dai sauransu.”

Honorabul Bello ya ja hankalin matasa da su kasance jakadu nagari a kodayaushe wajen bin dokoki da tsarin mulki, kana su guji ta’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma mutunta manya.

Hon. Bello ya kuma shawarci shuwagabannin ƙananan hukumomi 27 da su fara aiwatar da shirye-shirye na mai girma Gwamna Zulum, su kasance masu riƙon amana ga jama’arsu.

Ya kuma shawarci shuwagabannin jam’iyyar na yankin su kasance jakadun jam’iyyar nagari a duk inda suke jagorancin jama’a.