Tsohon lauyan Trump ya ce uban gidansa ya ba ‘yar finafinan batsa toshiyar baki

Tsohon babban lauyan Donald Trump, Michael Cohen, ya aikata abinda masu gabatar da ƙara su kai ta fatan ya aikata, na bayar da bayanan da suka tabbatar da tuhume-tuhumen da suka gabatar wa kotu.

Shaidar da Cohen, ya bayar dai ta ƙara tabbatar da zargin masu gabatar da ƙara na alaƙar Trump da Stormy Daniels.

A baya dai an zargi Trump ɗin da yin lalata da Stormy Daniel, kuma ya biya ta maƙudan kuɗaɗen toshiyar baki, don kar ta fallasa alaƙar da ke tsakaninsu.

Zargin da Trump ɗin ya rinƙa musawa a lokutan baya, ko da yake ana ganin yana yin hakan ne don yaƙin neman zaɓensa na shugabancin ƙasar da ke tafe.

Yanzu haka dai Cohen, ya tabbatar da cewa an tura wa Stormy Daniels maƙudan kuɗaɗen.

Sai dai a cewarsa, bai ɗauki ko wanne mataki ba sai da ya sami izini daga Trump kafin ya kai ga biyan Stormy maƙudan kuɗaɗen.