Majalisar Dattawa ta amince da kafa Hukumar Raya Arewa maso Yamma

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne Majalisar Dattijai ta amince da ƙudirin dokar Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma domin magance ƙalubalen da jihohi bakwai ke fuskanta a yankin.

Wannan ya biyo bayan la’akari da amincewa da rahoton Kwamitin Ayyuka na Musamman akan NWDC ya yi.

Ƙudirin dokar wanda ya wuce karatu na uku a majalisar ya samu ɗaukar nauyin mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau Jibrin, da wasu ’yan majalisa 20 daga jihohi bakwai na shiyyar Arewa maso Yamma.

Shugaban kwamitin Sanata Shehu Kaka (mai wakiltar Borno ta tsakiya) wanda ya gabatar da ƙudirin, ya ce an tsara ƙudirin ne bisa dabarun bunƙasa zamantakewa da tattalin arzikin yankin Arewa maso yamma.

Ya kuma ƙara da cewa kafa hukumar zai qara kusantar Gwamnatin Tarayya da jihohin Arewa maso Yamma da kuma biyan buqatun jama’a.

Bayan kafa Hukumar Raya Neja-Delta (NDDC) da Hukumar Cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC), wasu shiyyoyin ƙasar sun fara neman kwamitocinsu.
An kafa hukumar NEDC ne biyo bayan ɓarnar da mayaƙan Boko Haram suka yi a yankin Arewa maso Gabas.

Ana kuma shirin kafa hukumar raya yankin kudu maso gabas.

By Editor