Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wato babbar matsalar mu ita ce yadda akasari ba ma iya kallon abubuwa ta mahangar zahiri sai dai ta mahangar son rai kawai. A yan kwanakin nan na yi mamakin irin yadda wannan dabi’a ta mamaye mu, domin na tattauna da matasa, mata, manyan mutane da dama har da Farfesoshi da malamai, amma akasari mun kasa fahimtar cewa a zaben 2027 sai dai wani kadaru na Allah kawai zai iya hana Tinubu zarcewa a 2027.
Ku bi ni a hankali da idon basira zan yi muku bayani dalla-dalla yadda za ku iya gamsuwa da hasashe na. Na farko shine a fara gane cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanede-tanade guda biyu wadanda dole sai dan takarar shugagan kasa ya hada su, sannan zai iya darewa karagar mulkin Najeriya.
Na farko shine cewa dole sai dan takarar ya ci kaso 25% na kuri’a da aka kada a jihohi 2/3 na Najeriya. Jihohi 2/3 na Najeriya kuma shine jiha 24 cif. Idan ba mu manta ba, a zaben 2023, Tinubu ya ci wadannan jihohi. Duk da cewa an so kawo kalubalen cewa akwai Abuja, amma ba ta kai matsayin jiha ba, abinda sai da ya kai ga Supreme Court wadda ta fassara cewa to, ko dai mutum ya ci jihohi 23 tare da Abuja ko kuma ya ci jihohi 24 ba tare da Abuja ba, kamar yadda Tinubu ya yi a 2023. Sharadi na biyu shine ko ka ci wadancan jihohi, sai kuma ka zarta samun kuri’u, ko da da guda daya ce a duk kuri’un da aka kada.
Ganin yadda Tinubu ya tsallake 2023 da kyar, wato samun iya kason jihohi 24 da kuma ganin cewa kuri’ar yan adawa a jumlatan sun haura nasa da sama da miliyan 4, ya sa ya shigo gwamnati da shirin gaske wajen ganin cewa lallai ya samu tazarce a 2027. Wanna dalili ya sa ya na hawa mulki ya cire tallafin mai, abinda ya ba shi damar tarawa gwamnatoci makudan kudade tare da talauta talakawan kasar.
Sannan ya fara farautar Gwamnoni su shiga APC yadda a yau ya kafa tarihin gwamnatinsa ce ta fi kowacce a baya yawan gwamnoni da ke jam’iyyarsa. A yanzu akwai jihohi 31. Dan uwa in tambaye ka tsakani da Allah, ka na tsammanin akwai wani gwamna a Najeriya da ke cikin gwamnonin APC 31 wanda zai gaza samawa Tinubu kashi 25% kacal na kuri’ar da aka jefa a jiharsa? Kana tsammanin cewa Tinubu zai tsaya ne kawai a kan jihohi 24 wadanda ya ci kaso 25% a 2023?
Idan ka juwa bangaren adawa, a yanzu akwai Atiku, Obi da Jonathan a jam’iyyu uku na ADC, NDC da PDP. To ko rantsuwa ka yi ba za ka yi kaffara bai dan kace duk cikinsu ba wanda zai iya kawo kaso 25% a jihohi 24. Domin a baya ma lokacin da Atiku ke da gwamnoni 13, da kyar Atiku ya iya samun kaso 25% a jihohi 21. Peter Obi ya samu a jihohi 16. A yau da ba wanda cikinsu ke da gwamna daya, akwai yiwuwar su iya samun kason a jihohi 24?
Sannan idan ka koma maganar yawan kuri’a, Atiku ba zai iya samun kuru’in da ya samu a baya ba, haka shi ma Peter Obi, musamman shigo da Jonathan cikin lissafin. Yan adawa, ba makawa sun sake tafka kuskuren da su ka yi a 2023 (said ai in kuma da ma shugaba Tinubu su ke wa aiki kamar yadda Malam Shekarau ya ambata). Don haka wajibi ne kuri’ar Tinubu ta zarta ta kowanne dan Takara da zai kara da shi a 2027.
Kun ga tun kafin zabe, ya cinye zaben, sai dai kuma babu wanda ya san mai zai faru an jima ballantana gobe, kuma kana ta kulle-kullenka, mu na ta hasashe-hasashen mu, Allah ne kadai ya san me zai faru gobe.
Allah ka iya mana ba don iyawarmu ba! Ka wayar da mu, yadda talaka zai gane karfinsa ya Kuma yi amfani da shi wajen rusa azzaluman Yan siyasa da su ka bautar da shi.
Jumu’a Mubarak.
Malam Ali ya wallafa ne a shafinsa na Faecbook
