Gwamnan Zamfara na cikin tawagar da za ta wakilci Nijeriya a taron zuba jari na Kanada-Afirka

Spread the love

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, tare da wasu gwamnoni da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa za su wakilci Nijeriya a taron ƙoli na Kanada-Afirka kan hanyoyin zamani na tattalin arziki da za a gudanar a Toronto kamar yadda sanarwar ta fito daga mai magana da yawun gwaman Sulaiman Bala Idris.

Taron zuba jari na farko na irin sa zai gudana ne daga ranar 10 zuwa 15 ga Agusta, 2026, a birnin Toronto na ƙasar Kanada.

A cikin wasiƙar gayyatar da fadar shugaban ƙasa ta aika wa gwamna Lawal, an bayyana cewa kasancewarsa cikin manyan mahalarta taron zai taimaka wajen ƙarfafa matsayin Nijeriya ta fuskar diflomasiyya da tattalin arziki, musamman a dandalin taron zuba jari da tattalin arzikin ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje, wato Nigeria Diaspora Investment Economic Conference (NDIEC).

NDIEC na daga cikin manyan dandamalin ƙasa da ƙasa da ke haɗa gwamnatoci, masu zuba jari, manyan kamfanonin ƙasa da ƙasa, cibiyoyin ba da tallafin kuɗaɗen raya ƙasa, gidauniyoyi da sauran abokan hulɗa domin ƙulla dabarun haɗin gwiwa da gano damarmakin zuba jari.

Gwamnatin Zamfara ta ce, taron zai taimaka wajen ciyar da manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu gaba, musamman ta hanyar tsarin sauyin makamashi na ƙasa, wanda ke da nufin bai wa Nijeriya damar taka muhimmiyar rawa a haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin Afirka da Kanada.

A cewar gwamnatin jihar, NDIEC ba taron diflomasiyya kawai ba ne, illa wata muhimmiyar tafiya ce ta tattalin arziki da za ta ba Zamfara damar jawo zuba jari, sauya fasahar zamani zuwa cikin gida, samun tallafin kuɗaɗen raya ƙasa da kuma ƙulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwar fasaha domin sauya fasalin tattalin arzikin jihar.

Ta ce halartar Gwamna Lawal a taron zuba jari na Kanada da Afirka zai taimaka wajen fito da Zamfara a matsayin ɗaya daga cikin cibiyoyin da ke tasowa a Nijeriya wajen kasuwancin noma da sarrafa amfanin gona, bunƙasa ma’adinai masu muhimmanci, haɓaka ƙwarewar jama’a da kuma ƙirƙire-ƙirƙiren zamani na dijital.

Sauran wakilan Nijeriya a taron sun haɗa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo; gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum; gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani; da gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang.

Haka kuma tawagar ta ƙunshi ministar harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu; ministar masana’antu, ciniki da zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole; da ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, da sauran manyan jami’an gwamnati.

By ukarofi

Leave a Reply