
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla mutane 13 ne aka ceto bayan wani gida ya rushe a yankin Ɗan Dishe da ke Kwanar Yashi a Ƙaramar Hukumar Fagge ta jihar Kano, a safiyar ranar Asabar.
Haka kuma, wasu mutane 16 sun samu raunuka sakamakon faruwar al’amarin.
Hukumar Kashe Gobara ta jihar ta ce sashenta na bayar da agajin gaggawa ya samu kiran gaggawa kan iftila’in da misalin ƙarfe 4:32, wanda ya sa cikin hanzari ta tura jami’ai daga hedikwatarta zuwa wajen domin kai ɗauki.
Jami’inta na hulɗa da jama’a, Saminu Abdullahi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
A cewarsa, ginin da ya rushen ya kasance mai girman jimillar kafa 20 zuwa 30, inda ya ƙara da cewa an ceto mutane 13 daga cikin baraguzansa, waɗanda daga ciki, 10 babu abin da ya same su, sa kuma sauran ukun an same su cikin halin ɗimuwa.
Waɗanda aka ceto a rayen sune Al-Mustapha Yusuf mai shekara 15, Khadija Yusuf, shekara 7, Ummusalama Yusuf (10), Madina Yusuf (6) da kuma Hafsat Yusuf (9).
Hukumar ta kuma bayyana sunayen sauran ukun da suka galabaita, waɗanda sune Affan Yusuf (shekara 5); Hassana Yusuf, (7); da kuma Ummulkursum Yusuf (‘yar wata tara). Ta ƙara da cewa, sauran takwas ɗin da aka ceto ba a iya gano sunaye da shekarunsu ba a nan take.
Hukumar ta ce, ba a gano ainihin abin da ya sabbaba faruwar al’amarin ba, saidai ana cigaba da gudanar da bincike a kai.
A ƙarshe, hukumar ta yi kira ga al’umma da su riƙa ɗaukar matakan kariya tare da ruwaito dukkan wata alama ta rauni ga hukumomin da suka dace domin kare aukuwar irin haka a gidaje ko wuraren harkokinsu na yau da kullum.
