Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Osun kuma ɗan takarar Jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agusta, Ademola Adeleke, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa zai sake lashe zaɓe idan aka gudanar da shi cikin sahihanci da adalci.
Adeleke ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wani gangamin neman zaɓen tazarce da aka gudanar a Osogbo.
“Da taimakon Allah, ina da cikakken yaƙinin samun nasara. Idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, zan yi nasara,” inji shi.
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa ana kashe mambobin jam’iyyarsa, lamarin da ya sa ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya umarci rundunar ‘yan sanda ta gudanar da aikinta cikin ƙwarewa da nuna rashin son kai yayin zaɓen.
“Maigirma Shugaban ƙasa, akwai abin da ke faruwa a Osun da ya kamata ka sani. Ana kashe mutanenmu, kuma muna roƙonka a matsayinka na uba da ka ɗauki mataki.
“Ba za mu amince da duk wani yunƙurin maguɗin zaɓe ba, kuma kada a bari a ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Ka umarci ‘yan sanda su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da adalci. Kai ka yi gwagwarmayar tabbatar da dimokuraɗiyya, don haka kada ka bari wani ya lalata ta,” inji shi.
Adeleke ya ce idon ƙasashen duniya na kan zaɓen Osun, yana mai cewa za a yi amfani da shi wajen auna yadda babban zaɓen shekarar 2027 zai kasance.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su fito kwansu da kwarkwatarsu ranar zaɓe domin kaɗa masa ƙuri’a tare da kare ƙuri’unsu har zuwa lokacin da za a sanar da sakamakon zaɓen.
“Ina kira ga dukkan magoya bayanmu da su fito ranar 15 ga Agusta su zaɓe ni, sannan su tsaya tsayin daka wajen kare ƙuri’unsu har sai an bayyana sakamako. Na shirya tsaf domin wannan zaɓe, kuma juyin juya halinmu zai kasance ne ta akwatin zaɓe,” inji shi.
