Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.87 a 2025 — CBN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa tattalin arzikin cikin gida na ƙasar ya bunƙasa da kashi 3.87 cikin ɗari a shekarar 2025, idan aka kwatanta da kashi 3.38 cikin ɗari da aka samu a shekarar 2024.

Hakan na ƙunshe ne cikin Rahoton Shekara na 2025 da bankin ya wallafa, inda ya danganta wannan ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki a muhimman fannoni, tare da sake fasalin tsarin ƙididdigar tattalin arzikin ƙasar domin haɗa sabbin sassan da suka fara taka rawa.

Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 15.15 cikin ɗari a watan Disamban 2025, daga kashi 34.80 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2024.

A cewar CBN, wannan sauyi ya samo asali ne daga tsaurara manufofin kuɗi, daidaituwar darajar musayar kuɗi, da kuma sabon tsarin ƙididdige Ma’aunin Farashin Da Ake Buƙata (CPI).

Bankin ya ce sabon tsarin ya sake tsara nauyin kayayyakin da ake amfani da su wajen ƙididdige CPI domin ya fi dacewa da yadda gidaje ke kashe kuɗaɗensu a halin yanzu.

CBN ya kuma bayyana cewa kuɗaɗen shiga Asusun Tarayya sun ƙaru da kashi 33.67 cikin ɗari a shekarar 2025, sakamakon ƙarin kuɗaɗen shiga daga man fetur da kuma sauran hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ba tare da dogaro da mai ba.

Rahoton ya ce wannan ci gaba ya ƙara yawan rabon kuɗaɗe ga matakan gwamnati uku, lamarin da ya taimaka wajen ƙarfafa ɗorewar harkokin kuɗaɗen gwamnati.

CBN ya danganta wannan da ƙaruwar kuɗaɗen harajin ribar kamfanonin mai, Harajin ɓAT da kuma harajin ribar kamfanoni.

Rahoton ya nuna cewa zuwa ƙarshen watan Satumban 2025, jimillar bashin gwamnati ya kai Naira tiriliyan 153.29, wanda ya yi daidai da kashi 35.55 cikin ɗari na GDP.

By ukarofi

Leave a Reply