‘Yan bindiga sun buƙaci fansar miliyan N50 bayan sace malama a Nasarawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun yi awon-gaba da wata malamar makaranta mai suna Amina Hussaini daga gidanta de ke yankin Kuru a Ƙaramar Hukumar Toto da ke Jihar Nasarawa, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.

Wata ‘yar gidansu malamar mai suna Suwaiba Abdullahi ce ta tabbatar da labarin ga manema labarai ta wayar tarho a ranar Alhamis. Ta ce, an sace malamar, wadda ke karantarwa a makarantar firamare ta LEA Primary School da ke Kuru ne a ranar Talata a lokacin da mijinta ya tafi Lafii wani aiki. A cewarta, masu garkuwar sun kira ‘yan gidansu bayan aukuwar lamarin inda suka nemi a biya Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansar sako malamar.

Ta bayyana cewa, wannan al’amari ya tayar da hankalin ‘yan gidan nasu kan yadda za su samo waɗannan maƙudan kuɗaɗen. Sannan, ta ce a lokacin da ɗaya daga cikin ‘yan gidan nasu ya nemi su rage adadin kuɗaɗen, sai suka katse kiran cikin fushi.

Suwaiba Abdullahi ta ƙara da cewa malamar tana hannun ‘yan bindigar a halin yanzu yayin da suka sanar da ‘yan sanda, tana mai cewa iyalan suna roƙon al’umma da su taimake su wajen ceto ‘yar uwar tasu.

Kazalika, ta yi kira ga masu faɗa-a-ji, hukumomin tsaro da gwamnatin jihar Nasarawa da su shiga tsakani domin a samu sako malamar cikin aminci. Yayin da aka nemi ji ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce ya samu rahotannin garkuwar a Soshiyal Mediya kuma za su yi bincike tare da fitar da bayani a kai a nan gaba.

By Babaji

Leave a Reply