’Yan sanda sun gargaɗi ’yan siyasa kan tashin hankali yayin kamfen

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani nau’in daba, tashin hankali da sauran ayyukan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya yayin gudanar da kamfen ɗin zaɓukan da ke tafe.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ali Umar Fage, ya ce rundunar a shirye take, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi da kuma gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, rundunar ta jaddada cewa kowa na da ’yancin shiga harkokin kamfen da zaɓe, amma dole ne a gudanar da hakan bisa tanadin doka.

Rundunar ta ce ba za ta lamunci daba da tashin hankalin siyasa, kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a, lalata allunan tallan ’yan siyasa da fastoci, tarukan da ba su da izini, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, sayen ƙuri’u ko duk wani aiki da zai iya kawo barazana ga zaman lafiyar jama’a ba.

CP Ali Umar Fage ya kuma yi gargaɗin cewa rundunar za ta ɗauki matakin da ya dace kan duk wani mutum ko ƙungiyar da aka samu tana karya dokar zaɓe ko wasu dokokin ƙasa, ba tare da la’akari da matsayinsa ko jam’iyyar siyasar da yake goyon baya ba.

Rundunar ta buƙaci iyaye, masu kula da yara, ’yan takara da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da su gargadi ’ya’yansu, magoya bayansu da ’yan jam’iyyunsu kan shiga ayyukan da suka saɓa wa doka.

Haka nan kuma, ta shawarci ’yan takara da su gudanar da kamfen ɗinsu bisa ƙa’idojin da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC, ta shimfiɗa.

Rundunar ta buƙaci jama’a da su kasance masu bin doka tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da yanayin da zai bai wa dukkan ’yan takara da jam’iyyun siyasa damar gudanar da harkokinsu cikin adalci da kwanciyar hankali.

By ukarofi

Leave a Reply