2027: APC ta dage kan Uzodimma duk da hukuncin kotu ga Okorocha

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jam’iyyar APC a Jihar Imo ta dage cewa Gwamna Hope Uzodimma ne ɗan takararta na kujerar Sanatan Imo ta Yamma a zaɓen shekarar 2027, duk da hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke na amincewa da tsohon gwamnan jihar, Rochas Okorocha, a matsayin halastaccen ɗan takarar jam’iyyar.

Jam’iyyar ta bayyana matsayarta ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na jihar, Onwuasoanya Jones, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, bayan hukuncin da Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke.

Kotun ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ta saka sunan Okorocha a matsayin ɗan takarar APC na kujerar sanatan gundumar. Haka kuma, ta umarci Uzodimma da ya daina gabatar da kansa a matsayin ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairun 2027.

Sai dai jam’iyyar APC ta yi watsi da wannan matsaya, inda ta jaddada cewa Uzodimma ne ɗan takararta, bisa hujjar cewa ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da gagarumin rinjaye daga cikin mambobinta.

Sanarwar jam’iyyar ta ce, “Jam’iyyar na son bayyana ba tare da wani ruɗani ba cewa Mai Girma Sanata Hope Uzodimma, CON, shi ne ɗan takararmu na kujerar Sanatan Imo ta Yamma, bayan ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyarmu tare da gagarumin goyon bayan mafi yawan mambobinta.”

APC ta kuma bayyana cewa sashen shari’arta zai yi nazari kan hukuncin kotun kafin yanke shawarar matakin da za ta ɗauka na gaba. Sanarwar ta ce, “Sashen shari’ar jam’iyyar zai nazarci sakamakon wannan matakin shari’a da aka ɗauka kan batun, sannan ya ɗauki matakin da ya dace.”

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga mambobinta da magoya bayanta da su kwantar da hankulansu, su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da nasarar APC a dukkan gundumomin zaɓe na jihar.

Rikicin ya samo asali ne daga zaɓen fidda gwani na APC na kujerar sanatan Imo ta Yamma da aka gudanar ranar 18 ga Mayun 2026. Bisa sakamakon da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta amince da shi, an ayyana Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ƙuri’u 230,464, yayin da Okorocha ya samu ƙuri’u 1,098.

Bayan haka, Okorocha ya garzaya kotu domin ƙalubalantar sakamakon, yana hamayya da amincewa da Uzodimma a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, kotun ta ce Okorocha ne halastaccen wanda ya lashe zaɓen fidda gwani. Saboda haka, ta umarci APC da ta miƙa sunansa ga INEC domin a amince da shi a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

Kotun ta kuma nuna damuwa kan saɓani da rashin daidaito da ta gano a wasu takardun da jam’iyyar ta gabatar domin tabbatar da zaɓen Uzodimma a matsayin ɗan takara.

Duk da wannan hukunci, APC ta ci gaba da dagewa cewa Uzodimma ne ɗan takararta, tana mai cewa za ta nazarci hukuncin ta hannun sashen shari’arta kafin yanke matakin da za ta ɗauka.

By ukarofi

Leave a Reply