Koƙarin Tinubu na tabbatar da sahihin zaɓen 2027

Spread the love

Da alama Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ba ya son barin komai ga sa’a wajen tabbatar da gudanar da zaɓukan shekarar 2027 cikin ’yanci, adalci, gaskiya da karɓuwar al’umma.

Umarnin da ya bai wa shugabannin hukumomin tsaro na rusa sansanonin ’yan ta’adda da ’yan bindiga, kuɓutar da ’yan Nijeriya da aka sace, da kuma ƙarfafa tsaro gabanin zaɓukan watan Janairu, ya ƙara tabbatar da wannan ra’ayi. Haka kuma, matakin ya nuna irin ƙudurin gwamnatin Tinubu da ta sha nanatawa na ganin an gudanar da zaɓukan cikin nasara.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ne ya bayyana hakan a makon da ya gabata, yayin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban ƙasa bayan wani taron tsaro da Shugaba Tinubu ya jagoranta a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja.

An gudanar da taron ne domin yi wa shugaban ƙasa bayani kan halin da tsaro ke ciki a faɗin ƙasar, tare da duba matakan da ake ɗauka gabanin zaɓukan. A yayin taron, an kuma umarci shugabannin hukumomin tsaro da su tabbatar da samar da yanayin tsaro da zai bai wa ’yan Nijeriya damar shiga zaɓukan cikin ’yanci ba tare da fargaba ba.

A cewar ministan, dukkan shugabannin hukumomin tsaro sun halarci taron, inda Tinubu ya jaddada muhimmancin gudanar da zaɓe cikin ’yanci, adalci da sahihanci.

Janar Musa ya ce, shugaban ƙasar ya bayyana ƙarara cewa yana son a gudanar da zaɓe mai inganci, kuma wajibi ne a yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaron ƙasa, domin ’yan ƙasa su fita su kaɗa ƙuri’unsu cikin kwanciyar hankali.

Ministan Tsaron ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa jami’an tsaro za su kasance masu tsaka-tsaki a lokacin zaɓe, kuma ba za su lamunci duk wani yunƙuri na tsoratar da ’yan siyasa ko masu kaɗa ƙuri’a ba. Ya bayyana cewa za a bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar shiga zaɓen ba tare da fuskantar cin zarafi ko barazana ba.

Janar Musa ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su fahimci cewa jami’an tsaro za su gudanar da ayyukansu cikin adalci, ba tare da nuna bambanci ba. Haka nan, ya buƙaci ’yan Nijeriya su ba hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar sanar da su muhimman bayanai da za su taimaka wajen hana aikata laifuffuka da inganta tsaron al’umma.

Ministan ya ƙara da cewa, shugaban ƙasa ya umarci hukumomin tsaro da su ƙara zafafa ayyukansu domin kuɓutar da mutanen da aka sace, tare da rusa sansanonin ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar.

A cewarsa, umarnin ya wajabta wa hukumomin tsaro su yi duk mai yiwuwa wajen gano inda aka ɓoye waɗanda aka sace da kuma kuɓutar da su, ko da kuwa a ina ake tsare da su.

Ya ce umarnin shugaban ƙasa a bayyane yake: dole ne jami’an tsaro su tashi tsaye wajen gano duk mutanen da aka sace tare da kuɓutar da su, kuma kada a bar wani sansanin ’yan ta’adda ko ’yan bindiga a ko ina a Nijeriya.

Musa ya kuma yi watsi da iƙirarin cewa ana ɗaukar yara ƙanana aiki a rundunar sojin Nijeriya. Ya bayyana cewa damuwar da aka nuna game da amfani da yara wajen ayyukan yaƙi ta shafi ’yan ta’adda ne, ba rundunar sojin ƙasar ba.

Ya ce gwamnati ta himmatu wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da kuma hana su ci gaba da samun sansanonin gudanar da ayyukansu a cikin ƙasar.

Dangane da ƙoƙarin ƙarfafa ƙarfin hukumomin tsaro, ministan ya bayyana cewa gwamnati na ƙara ɗaukar ma’aikata, horas da su da kuma sayen kayan aikin soji.

Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba, Shugaba Tinubu zai ƙaddamar da wasu sabbin jiragen sama da jirage masu saukar ungulu guda kusan 10 da aka saya domin inganta ayyukan soji.

A cewarsa, shirin ƙaddamar da jiragen ya nuna cewa gwamnatin Tinubu na ci gaba da bai wa harkokin tsaro muhimmanci, duk da ƙalubalen tattalin arzikin da ƙasar ke fuskanta.

Musa ya kuma yi nuni da ƙarin albashin da aka yi wa jami’an rundunonin soji a baya-bayan nan, inda ya ce ana kuma ɗaukar matakan inganta walwalar ’yan sanda, ma’aikatan sauran hukumomin tsaro da masu karɓar fansho. Ya tabbatar da cewa gwamnati na son tabbatar da cewa waɗanda ke da alhakin kare ƙasa sun samu ingantacciyar kulawa da walwala.

Ministan ya sake jaddada cewa tsaro nauyin kowa ne, tare da kira ga ’yan ƙasa da su riƙa kai rahoton ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka ga hukumomin da suka dace. Ya kuma buƙaci a kai rahoton duk wani rashin da’a ko cin zarafi da jami’an tsaro suka aikata ga hukumomin da abin ya shafa, yana mai tabbatar da cewa za a ɗauki matakin da ya dace.

Bugu da ƙari, jim kaɗan bayan ganawarsa da shugabannin hukumomin tsaro, ministan ya bayyana cewa Tarayyar Turai na shirin bai wa Nijeriya tallafin tsaro na yuro miliyan 20 domin taimaka wa rundunonin sojin ƙasar wajen yaƙi da matsalar rashin tsaro. Ya ce za a bayar da tallafin ne ƙarƙashin shirin Asusun Zaman Lafiya na Turai, inda wata tawagar ƙwararru daga Tarayyar Turai za ta ziyarci Abuja a watan Nuwamba domin cimma matsaya kan yadda za a gudanar da shirin.

A ra’ayin jaridar Blueprint Manhaja, ƙudurin da Shugaba Tinubu ke nunawa na tabbatar da samar da yanayin tsaro da zai bai wa duk wani ɗan Nijeriya da ya cancanta damar shiga zaɓukan shekara mai zuwa abin a yaba ne matuƙa. Wannan mataki na da muhimmanci wajen hana tauye wa wasu ’yan ƙasa ’yancin kaɗa ƙuri’a, musamman waɗanda ke zaune a yankunan da suka fi fama da ayyukan ’yan bindiga da ta’addanci, kamar Arewa maso Yamma, Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya.

Wannan ƙuduri kuma shaida ce da ba za a iya musantawa ba kan irin martabar dimokuraɗiyyar da shugaban ƙasar ke son ginawa. Sai dai, bayan bayar da wannan umarni, nauyin tabbatar da aiwatar da shi ya rataya ne a wuyan shugabannin hukumomin tsaro. Rusa sansanonin ’yan ta’adda da ’yan bindiga kafin zaɓukan shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta ƙasa da aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027, wanda ya rage ƙasa da watanni uku, ba ƙaramin ƙalubale ba ne.

Duk da haka, idan aka haɗa ƙarfi da ƙarfe, hukumomin tsaro suka jajirce, tare da samun goyon bayan ƙasashen duniya, ciki har da tallafin yuro miliyan 20 da Tarayyar Turai ta yi alƙawarin bayarwa, ya kamata ’yan Nijeriya su kasance da kyakkyawan fata cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan matsalar rashin tsaro a faɗin ƙasar. Wannan fata bai kamata ya tsaya ga lokacin zaɓen 2027 kaɗai ba, sai dai ya zama burin da za a ci gaba da tabbatarwa bayan zaɓukan.

A ƙarshe, gudanar da sahihin zaɓe ba ya dogara ga kyakkyawar niyya ko umarnin shugabanni kawai. Yana buƙatar aiwatar da matakan tsaro yadda ya kamata, tabbatar da zaman tsaka-tsaki na jami’an tsaro, da kuma kare haƙƙin dukkan masu kaɗa ƙuri’a. Saboda haka, abin da ’yan Nijeriya ke buƙata yanzu shi ne ganin an sauya waɗannan alƙawura zuwa ayyukan zahiri, domin a gudanar da zaɓen 2027 cikin aminci, ’yanci da gaskiya.

By ukarofi

Leave a Reply