
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano, ta ce ta daƙile wani yunƙuri na yi garkuwa a Ƙaramar Hukumar Gezawa da ke jihar kuma ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a barazanar sace wani mai gari.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an da ke aiki a babban ofishin hukumar Gezawa Division ne suka kama mutum biyun bayan samun wasu bayanan sirri na barazanar yin garkuwa da mai garin Bangare, Mallam Idris.
A cewar sanarwar da Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, mai garin ya shigar wa ‘yan sanda ƙorafin barazanar tun a ranar 26 ga Oktoba, 2026. Ya ce, Mallam Idris ya samu labarin barazanar ne ta wata kiran wayar tarho a ranar 24 ga Oktoba da misalin ƙarfe 9:33 na dare daga wani da bai san ko waye ba da ke barazanar yin awon-gaba da shi.
Bayan samun ƙorafin ne jami’an Gezawa Division suka fara ƙoƙarin gano yadda al’amarin yake bisa ƙwarewar aiki, lamarin da ya taimaka aka kama waɗanda ake zargin, kamar yadda sanarwar ta bayyana. ‘Yan sandan sun kuma ce mutanen sun amsa laifinsu, sannan ana cigaba da gudanar da bincike a kai yayin da ake shirin gurfanar da su a kotu.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da nuna ƙwarewa tare da jinjina ga ƙoƙarinsu na daƙile zargin shirin garkuwar, yana mai jaddada aniyarsu ta nuna ba-sani-ba-sabo ga masu aikata miyagun laifuka da kuma muhimmancin bayanan sirri wajen kare aikata su.
Akan haka ne rundunar ta kirayi mazauna da su cigaba da kasancewa masu lura da ƙoƙarin ruwaito dukkan wani abin zargi da suka gani a yankunansu akan kari ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa domin taimaka wa ayyukan ƙarfafa tsaro a jihar.
