Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Shugaban ƙaramar hukumar Koko-Besse, Honarabul Sirajo Usman Koko ya ziyarci ’yan gudun hijira da suka fito daga ƙauyukan Waiwayi da Kyastu da kuma Luka daga ƙaramar hukumar Shanga da ke maƙotaka da karamar hukumar Koko da ke jihar Kebbi, sakamakon haren haren da ake yawan kai musu.
A yayin ziyarar, bayan ya jajenta musu ya kuma buƙaci da su zauna lafiya da juna tare da tabbatar musu da isar da koken damuwar su ga gwamna Nasir Idris don ganin an saka su cikin shirin gwamnati na samar da tallafin gaggawa domin rage raɗadin halin da su ke ciki. Honarabul Koko ya raba tallafin gaggawa ga yan gudun hijirar a matakin karamar hukumar mulki wanda ya ce kuma in sha Allahu ba da dadewa ba tallafi zai zo daga gwamnatin jiha saboda ba za su zauna ba har sun ga mutanen sun fara samun walwala.
Ya kuma yi kira ga sauran al’umma da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai wajen kai rahoton duk wani mutum ko gungun mutane da ba su yarda da su ba saboda aikin tsaro bai tsaya ga ma’aikata ba kaɗai ya shafi kowa.
Wannan ba shakka ba ƙaramin bala’i ba ne a hana mutum zama lafiya a cikin aminci har ta kai ga a tilasta wa mutum da iyalan sa barin garin sa ya je wani gari a matsayin ɗan gudun hijira.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya kawo ƙarshen wannan masifa.
