(ƙarshe)
Daga AISHA ASAS
To idan haka ne, ta yaya mace za ta san abin da take shafawa?
A nan ne batun ya wuce kwalliya ya koma batun kariyar lafiya. Domin idan muka tambayi dalilin da ya sa mata ke amfani da kayan sauya launin fata, ba za mu samu amsa ɗaya ba. Wata mace tana neman kawar da tabon kuraje. Wata tana fama da canjin launin fata kuma tana son ya daidaita. Wata kuma tana ganin cewa fata mai haske ce ta fi kyau saboda abin da ta gani ko ta ji daga mutane. Wata kuma kawai tana bin abin da ƙawarta, ’yar uwarta ko wani mai tallata kayan kwalliya yake amfani da shi.
A ƙarshe, dukansu za su iya shiga shago ɗaya su sayi kwalba ɗaya, amma dalilin da ya kai kowacce cikinsu ya bambanta.
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce fahimtar waɗannan dalilai na da muhimmanci wajen magance matsalar amfani da kayan sauya launin fata. A sabon aikin da hukumar ta fitar a 2026, an jaddada muhimmancin fahimtar tasirin ra’ayoyin kyau, matsin lambar al’umma da tallace-tallace wajen fahimtar dalilin da ya sa mutane ke amfani da waɗannan kayayyaki.
A Najeriya ma wannan ba batun da za a ce na wasu ƙasashe ne kawai ba. Wani binciken da aka gudanar a Lagos a kan ’yan kasuwa 450 ya gano cewa kashi 77.3 cikin 100 na waɗanda aka bincika sun bayar da rahoton amfani da kayan sauya launin fata. Mata sun kasance mafi yawa cikin masu amfani da su, kuma kayayyakin da ke ɗauke da hydroƙuinone su ne suka fi yawa, yayin da corticosteroids da kayayyakin da ke ɗauke da mercury su ma an samu da dama. Sai dai wannan bincike na Lagos ne, kuma na rukunin mutanen da aka bincika ne; don haka ba hujja ba ce cewa kashi 77.3 cikin 100 na matan Najeriya suna amfani da mayukan bilicin ba.
Don haka bai kamace mace ta jira sai ta ga fatarta ta fara lalacewa kafin ta fara tambayar abin da ke cikin man da take shafawa ba. Maimakon haka tun daga lokacin da za ta saya ne ya kamata ta fara wannan tambayar. Ta karanta abin da aka rubuta a jikin kwalbar. Ta kula da sinadaran da ke ciki. Ta guji kayayyakin da ba su da cikakken bayani ko waɗanda ba a san asalinsu ba. Kuma idan tana da matsalar fata da take son magancewa, musamman kuraje, tabo ko sauyin launin fata, ta nemi shawarar likitan fata ko wani ƙwararren ma’aikacin lafiya maimakon ta fara haɗa magunguna da mayuka da kanta. Domin abin da muke kira “saurin aiki” na iya zama babbar matsala da za ta iya shafar lafiya.
Fata tana iya yi wa mutum kyau a yau, amma wasu illolin abin da aka shafa a kanta na iya bayyana daga baya. Kuma idan sinadarin da aka yi amfani da shi ya lalata fatar da ake ƙoƙarin kawatawa, to abin da aka fara da sunan kwalliya zai iya ƙarewa da neman magani.
Saboda haka, kyakkyawar fata ba ita ce kawai fata da ta fi haske ba. Kyakkyawar fata ita ce fata da take da lafiya, wadda ake kula da ita da abin da aka sani, ba da abin da kawai aka ce “yana aiki da sauri” ba.
Domin a lokacin da neman kyau ya fara jefa lafiyar fata cikin haɗari, tambayar da ta dace ba ita ce shin na yi kyau? ba ce. Tambayar ita ce: Wane farashi nake biya domin wannan kyawun?
