
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mazauna sun shiga firgici bayan wasu ‘yan bindiga sun afka wa Rukunin Gidajen Nurul Siraj da ke Unguwar Millennium City a Jihar Kaduna, inda suka yi awon-gaba da mutum shida a daren wayewar Talata.
Wani mazauni da ya nemi a sakaye sunansa, ya shaida wa Manhaja cewa maharan sun shiga rukunin gidajen ne ta ƙofa ta biyu, inda suka yi garkuwa da mazauna maza da mata. “Innalillahi wa’inna ilaihi Raji’oon. A daren da ya gabata ne masu garkuwa da mutane suka sace kusan mutane shida, da suka haɗa maza da mata a Nurul Siraj Estate, Millennium City, Kaduna ta ƙofa ta biyu,” inji shi. Ya kuma yi kria da a inganta tsaro a yanki tare da addu’ar kuɓutar waɗanda aka sace cikin aminci.
Wani rubutu da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna cewa an sace wani iyali da ya haɗa da uba, uwa da ‘ya’ya biyu da kuma wasu maƙota yayin harin. Haka kuma, an yi zargin cewa kimanin ‘yan bindiga 10 ne suka shiga wani gida suna neman wata mata saidai ba su same ta ba, lamarin da ya sa suka yi awon-gaba da ‘yan gidan da na wani gida.
Sannan, akwai rahotannin da ke cewa an yi musayar wuta tsakanin maharan da dakarun tsaro, amma duk da haka sai da suka tsere da wasu daga cikin mutanen da suka sace. Saidai Manhaja ba ta tabbatar da labarin ba yayin haɗa wannan rahoto. Babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Jihar Kaduna ko hukumomin tsaro game da al’amarin a yayin haɗa rahoton.
A ranar 6 ga Oktoba ne dai wannan jaridar ta ruwaito cewa wasu ‘yan bindiga sun yi awon-gaba da wani magidanci mai suna Ahmed Abubakar Zakka tare da matarsa da ‘yarsu mai wata shida, Fatima daga yankin Rukunin Gidajen Alrahus a Millennium City. Daga bisani ‘yan gidansu sun yi sanadiyyar ceto su.
