
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin bincike da Gwamnatin Tarayya ta kafa ya ce ya gano cewa mutane 37 da aka yi zargin masu aikin haƙar ma’adinai ne ba bisa doka ba, sun rasu a komar Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Ƙasa (NSCDC) a Jihar Neja ne a sakamakon rashin wadatacciyar iskar shaƙa. Ya ɗora alhaki akan cikowarsu a waje guda, rashin isashshiyar iska, matsin zafi, ƙishin ruwa da gazawar jami’an hukumar ga bayar da kariya da kulawar da ta dace a gare su.
Jonathan Kure, wato Shugaban kwamitin kuma Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) mai ritaya ne ya bayyana sakamakon binciken nasu ga Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo a Abuja, ranar Talata. A cewar kwamitin, da za a iya kauce wa aukuwar lamarin, amma aka samu gazawar kulawa da sanya ido kan halin waɗanda aka tsaren.
Ya bayyana cewa, sakamakon binciken likitoci kan gawarwakinsu bai nuna cewa ɓarkewar wata cuta ce ta yi ajalinsu ba kamar yadda aka yi iƙirari da fari. A madadin haka, ya gano cewa sun fuskanci ƙalubalen fafutukar numfashi a sanadiyyar cikowa da rashin wadatacciyar iska, inda daga bisani hakan ya yi silar rasuwarsu. Sannan sakamakon binciken ya haifar da wasu muhimman tambayoyi kan halin da aka tsare masu laifin kuma ko jami’ai sun yi amsawar da ta dace da suka nuna alamun suna buƙatar agajin gaggawa gabanin aukuwar mace-macen.
Waɗanda kwamitin ya yi hira da su kan iftila’in sun haɗa da jami’an NSCDC, masu kula da ɗakunan ajiye mai laifi, ma’aikatan lafiya, waɗanda suka tsira, iyalan mamatan da kuma wakilan al’umma. Haka kuma, ya yi nazari kan rajistar waɗanda aka tsare, rahotannin sadarwa, takardun asibiti da na gidan ajiyar gawarwaki, sakamakon rahoton binciken gawa da kuma rahotannin binne gawarwaki.
Har ila yau, rahoton ya kuma ce an yi wa mutum 29 daga cikin 41 da suka tsira tambayoyi, ciki har da wasu yara ƙanana su tara, yayin da kwamitin ke ƙoƙarin tattara bayanan haƙiƙanin abin da ya faru a lokacin. Kazalika, binciken ya gano cewa atisayen da jami’an na Sibil Difens suka gudanar da ya yi sanadiyyar kama masu haƙar ma’adinan bai samu izinin hukumar gudanarwa ko amincewar hedikwatar NSCDC ba.
A ranakun 15 da 16 ga Satumba, 2026 ne dai aka kama mutanen a lokacin da jami’an NSCDC suka kai samame a wuraren haƙar ma’adinai ba bisa doka ba da ke yankunan M.I. Wushishi da Lukoto a Minna, Jihar Neja. Sun rasu ne a ranar 17 ga Satumba bayan kwana biyu, yayin da suke tsare a ofishin NSCDC na jihar.
Bayan haka ne Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja, Suberu Siyaka Aniviye da wasu jami’ai 20 har zuwa lokacin kammala bincike. Gwamnatin ta kuma umarci hukumomi masu ruwa da tsaki da su bayar da haɗin kai ga bincike tare da tabbatar da cewa ba a samu wata rufa-rufa ba ga haƙiƙanin yadda al’amarin ya auku.
A ƙarshe, Shugaban kwamitin ya shawarci a bayar da Naira biliyan 1.4 a matsayin diyya ga iyalan mamata 33 da kuma mutum 44 da suka tsira. Ganin haka ya sa Ministan Cikin Gidan ya yi alƙawarin za a aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bada domin tabbatar da adalci ga dukkan waɗanda abin ya shafa.
