Cutar Ebola: Muhimman abubuwan da ya kamata a sani da hanyoyin kariya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tabbatar da samun ɓullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayyar ƙasar, wato Abuja, tare da fara aikin gano mutanen da suka yi mu’amala da wadda ta kamu da cutar, domin daƙile yaɗuwarta. Gwamnatin ta kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da su ƙara taka-tsantsan, su kiyaye matakan kariya tare da kai rahoton duk wata alama da ake zargin ta shafi cutar cikin gaggawa.

Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ne ya bayyana hakan ranar Talata, bayan gwaje-gwajen ɗakunan binciken lafiya sun tabbatar da kamuwa da cutar ga wata mata da ta shigo Nijeriya daga Uganda ta jirgin sama na ƙasa da ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa an kwantar da matar a wani asibiti mai zaman kansa da ke Babban Birnin Tarayya, inda ta shafe kwanaki tana karɓar magani kafin a tabbatar da cewa tana ɗauke da cutar. Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a halin yanzu an killace matar domin ba ta kulawar likitoci da ta dace. Haka kuma, an gano mutane 44 da suka yi mu’amala da ita ko kuma wataƙila sun fuskantar barazanar kamuwa da cutar. Mutanen sun haɗa da ma’aikatan lafiya, majinyata, masu kula da marasa lafiya da kuma mutanen da suka yi tafiya tare da ita.

ƙungiyoyin kula da lafiyar jama’a sun fara aikin gano wasu mutanen da ka iya fuskantar barazanar kamuwa da cutar, tare da sa ido kan lafiyarsu. Gwamnatin ta ce ta ƙara tsaurara sa ido kan cututtuka, tare da umartar asibitoci na gwamnati da masu zaman kansu da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, su hanzarta gano waɗanda ake zargin sun kamu da cutar da kuma killace su. Ta kuma buƙaci su bi ƙa’idojin kariya daga yaɗuwar cututtuka tare da sanar da hukumomin lafiya duk wani wanda ake zargi yana ɗauke da ita.

Ministan ya roƙi mutanen da jami’an lafiyar jama’a suka tuntuba, musamman fasinjojin da wataƙila suka yi tafiya tare da matar, da su ba da haɗin kai wajen gudanar da binciken gano waɗanda suka yi mu’amala da ita.

Biyo bayan tabbatar da ɓullar cutar a Abuja, an sake duba bayanan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) game da cutar Ebola da kuma shawarwarinta kan gano mutanen da suka yi mu’amala da masu ɗauke da cutar, domin wayar da kan ’yan Nijeriya game da yadda take yaɗuwa da matakan da za su taimaka wajen kare kansu.

Yadda cutar Ebola ke yaɗuwa:

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, mutum na iya kamuwa da cutar Ebola idan jini ko zufan jikin mutumin da ke ɗauke da cutar, ko wanda ya mutu sakamakon cutar, suka taɓa buɗaɗɗen rauni ko kuma wasu sassan jikinsa masu laushi, kamar cikin baki da idanu. Haka kuma, cutar na iya yaɗuwa ta hanyar taɓa kayayyaki ko wuraren da ruwan jikin mai cutar ya gurɓata, ciki har da jini, bayan gida da amai.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa mutumin da ya kamu da Ebola ba ya yaɗa cutar kafin alamominta su bayyana. Amma yana iya ci gaba da yaɗa ta muddin ƙwayar cutar tana cikin jininsa. Haka kuma, mutum na iya kamuwa da cutar ta hanyar mu’amala da dabbobin da suka kamu da ita, ciki har da wasu jemagu masu cin ’ya’yan itatuwa da namun daji. Wannan na iya faruwa musamman idan mutum ya taɓa dabbar da ta kamu da cutar ko kuma ya ci namanta. Saboda haka, hukumar ta shawarci jama’a da su guji taɓa namun daji marasa lafiya ko waɗanda suka mutu, sannan su guji cin namansu da bai dahu ba.

WHO ta kuma yi gargaɗin cewa ya kamata mutane su guji kusanci na zahiri da duk wanda ake zargin yana ɗauke da cutar ko aka tabbatar ya kamu da ita, musamman taɓa jini ko wasu ruwan jikinsa.

Ya kamata a killace waɗanda ake zargi sun kamu da cutar da waɗanda aka tabbatar sun kamu a cibiyoyin jinya da aka ware domin kula da su, inda za a iya ba su magani tare da aiwatar da matakan hana yaɗuwar cutar. Haka kuma, yana da muhimmanci mutane su riƙa wanke hannuwansu yadda ya kamata tare da tsaftace muhallinsu.

A gefe guda, ma’aikatan lafiya dole ne su yi amfani da kayan kariya na musamman tare da bin ƙa’idojin hana yaɗuwar cututtuka yayin kula da majinyatan da ake zargi suna ɗauke da Ebola ko waɗanda aka tabbatar sun kamu da ita. Wannan ya fi zama wajibi idan akwai yiwuwar taɓa jini, ruwan jiki ko kayayyakin da suka gurɓata.

Hukumar ta kuma jaddada muhimmancin gudanar da jana’iza cikin aminci da mutunta mamaci. Wasu al’adun jana’iza da suka haɗa da taɓa gawar mutumin da ya mutu sakamakon Ebola na iya jefa sauran mutane cikin haɗarin kamuwa da cutar.

Alamomin Ebola da lokacin da suke bayyana:

A cewar WHO, alamomin cutar Ebola na iya bayyana tsakanin kwanaki biyu zuwa 21 bayan kamuwa da ita. Alamomin farko sun haɗa da zazzaɓi, kasala, ciwon jiki, ciwon kai da ciwon maƙogwaro. Yayin da cutar ke ci gaba, mutum na iya fara amai, gudawa, ciwon ciki da wasu matsaloli na lafiya.

Sai dai hukumar ta yi gargaɗin cewa yana iya zama da wahala a bambance Ebola da wasu cututtuka, kamar zazzaɓin cizon sauro da taifod, ta hanyar duba alamomi kaɗai. Saboda haka, duk wanda ya fara nuna alamomin cutar bayan ya yi mu’amala da wanda ake zargin yana ɗauke da ita, ya nemi kulawar likitoci cikin gaggawa tare da sanar da su yiwuwar mu’amalar da ya yi. An kuma shawarci jama’a da kada su yi ƙoƙarin gano cutar ko kuma yi wa kansu magani a gida idan ana zargin sun kamu da ita.

Muhimmancin gano mutanen da suka yi mu’amala da masu cutar:

Gano mutanen da suka yi mu’amala da mai cutar, wanda aka fi sani da contact tracing a Turanci, wata hanya ce da hukumomin lafiya ke amfani da ita wajen gano mutanen da ka iya kamuwa da cutar daga hannun wanda ya kamu da ita, sannan su riƙa sa ido kan lafiyarsu.

A cewar WHO, wannan mataki yana taimakawa wajen tabbatar da cewa duk wanda alamomin cutar suka bayyana a jikinsa ya samu kulawar lafiya cikin gaggawa, tare da taimaka wa hukumomi daƙile ci gaba da yaɗuwar cutar.

Hukumar ta ba da shawarar a riƙa sa ido kan lafiyar mutanen da suka yi mu’amala da wanda ya kamu da cutar na tsawon kwanaki 21, domin wannan shi ne mafi tsawon lokacin da aka sani kafin alamomin Ebola su bayyana.

Duk wanda jami’an lafiyar jama’a suka tuntuɓa ya kamata ya bayar da sahihan bayanai tare da bin umarnin da suka ba shi. An kuma yi kira ga ’yan Nijeriya da suka yi zargin sun fuskanci barazanar kamuwa da cutar da su ba jami’an lafiya haɗin kai, maimakon ɓoye bayanai ko ƙin bin diddigin lafiyarsu.

Gwamnatin Tarayya ta kuma sanar da jama’a cewa za su iya kiran layin kyauta na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC) mai lamba 6232 domin samun bayanai ko kai rahoton waɗanda ake zargin sun kamu da cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa ba da kulawar lafiya cikin gaggawa, musamman maye gurbin ruwan jikin da aka rasa da kuma magance alamomin cutar, na iya ƙara wa majinyata damar tsira.

Saboda haka, kai rahoto da wuri, samun kulawar likitoci, ba da haɗin kai wajen gano mutanen da suka yi mu’amala da masu cutar da kuma bin ƙa’idojin kariya na da matuƙar muhimmanci wajen rage haɗarin ci gaba da yaɗuwar Ebola.

Abubuwa 20 da ya kamata a sani game da cutar Ebola:

1. Ebola cuta ce da ƙwayar cuta ke haddasawa. Cutar na faruwa ne sakamakon wasu ƙwayoyin cuta da ke cikin rukunin da masana kimiyya suka kira Orthoebolaɓirus.

2. An fara gano cutar Ebola a shekarar 1976. An fara samun ɓullar cutar da aka tabbatar a yankunan da a yau suka haɗa da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Sudan ta Kudu.

3. Cutar Ebola ta fi bayyana a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara. Yawancin ɓullar cutar da aka gano a hukumance sun faru ne a ƙasashen Afirka.

4. Ebola na iya haddasa mutuwa. Yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon cutar ya bambanta daga wannan ɓarkewar cuta zuwa wata. A wasu lokuta, adadin ya kai kashi 80 zuwa 90 cikin 100 ko ma fiye da haka, gwargwadon yanayin ɓarkewar cutar da sauran dalilai.

5. Kasancewa kusa da mai cutar ba ya nufin mutum zai kamu da ita kai tsaye. Tsayawa kusa da wanda ya kamu da Ebola, wucewa ta gabansa ko kasancewa tare da shi a wurin taron jama’a ba ya zama sanadin yaɗuwar cutar kai tsaye a yanayi na yau da kullum.

6. Ebola ba ta yaɗuwa ta iska kamar mura ko COɓID-19. Hanyar yaɗuwarta da aka fi sani ita ce taɓa ruwan jikin mai cutar kai tsaye ko taɓa kayayyakin da suka gurɓata da waɗannan ruwan jiki.

7. Cutar na yaɗuwa ta ruwan jikin wanda ya kamu da ita. Ruwan jikin da ka iya yaɗa cutar sun haɗa da jini, amai, bayan gida, fitsari, miyau, zufa, nonon uwa, maniyyi da ruwan farji.

8. Mai cutar yana fara iya yaɗa ta ne bayan alamominta sun bayyana. A cewar WHO, mutumin da ya kamu da Ebola ba a ɗauke shi a matsayin mai yaɗa cutar kafin alamominta su bayyana.

9. Lokacin da alamomin cutar ke ɗauka kafin su bayyana na iya kaiwa kwanaki biyu zuwa 21. A mafi yawan lokuta, alamomin cutar suna fara bayyana ne bayan kwanaki takwas zuwa 10 da kamuwa da ita.

10. Zazzaɓi na daga cikin alamomin farko na Ebola. Sauran alamomin farko sun haɗa da ciwon kai, ciwon tsoka, rauni da yawan gajiya.

11. Ebola na iya haddasa matsaloli masu tsanani a tsarin narkewar abinci. Yayin da cutar ke ƙara tsananta, majiyyaci na iya fama da amai, gudawa da ciwon ciki.

12. Zubar jini na iya faruwa a wasu lokuta masu tsanani. Wasu majinyata na iya zubar da jini ba tare da wani dalili bayyananne ba, amma ba lallai ne hakan ya faru ga duk wanda ya kamu da cutar ba.

13. Ebola na iya haddasa gazawar gabobin jiki. Idan cutar ta tsananta, tana iya lalata gabobin jiki da dama, tare da haddasa matsalar da ke sa jiki kasa samar da isasshen jini ga muhimman gabobinsa.

14. Ma’aikatan lafiya na cikin haɗarin kamuwa da cutar. Haɗarin yana ƙaruwa idan suna kula da masu cutar ba tare da kayan kariya da kuma bin ƙa’idojin hana yaɗuwar cututtuka yadda ya kamata ba.

15. ’Yan uwa da masu kula da marasa lafiya ma na iya kamuwa da cutar. Taɓa jinin ko wasu ruwan jikin mai Ebola ba tare da kiyaye matakan kariya ba na iya haddasa kamuwa da cutar.

16. Kayayyakin da suka gurɓata na iya yaɗa Ebola. Allurai, tufafi, shimfiɗar gado da kayan aikin asibiti da suka gurɓata da ruwan jikin mai cutar na iya zama hanyar yaɗuwarta.

17. Gudanar da jana’iza cikin aminci yana da matuƙar muhimmanci. Gawar mutumin da ya mutu sakamakon Ebola na iya ci gaba da kasancewa mai yaɗa cutar. Saboda haka, dole ne a bi ƙa’idojin kariya wajen taɓa gawar da gudanar da jana’izarta.

18. Dabbobi na iya zama tushen kamuwa da cutar. Mu’amala da wasu namun daji da suka kamu da cutar, ciki har da wasu nau’o’in jemagu da birai, na iya jefa mutum cikin haɗɗarin kamuwa da ƙwayoyin cutar Ebola.

19. Ana gano Ebola ta hanyar gwajin ɗakin binciken lafiya. Ana amfani da gwajin jini ta hanyar fasahar gano ƙwayoyin halitta da ake kira Polymerase Chain Reaction (PCR) wajen gano ƙwayar cutar a jikin mutumin da ke raye.

20. Duk wanda ake zargin ya kamu da Ebola yana buƙatar a duba lafiyarsa cikin gaggawa. Ya kamata a ware majiyyacin daga sauran mutane a cibiyar lafiya yayin da ake shirya gwaje-gwajen da suka dace da kuma matakan kariya daga yaɗuwar cutar.

By ukarofi

Leave a Reply