Harry Kane ya lashe kyautar Ballon d’Or ta 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kyaftin ɗin Ingila kuma ɗan wasan gaba na Bayern Munich, Harry Kane ya yi nasarar lashe kyautar karramawa ta Ballon d’Or ta maza ta 2026 a yayin babban taron karrama fitattun ‘yan wasan ƙwallon ƙafa da aka saba yi a kowace shekara. A gudanar da taron ne na bana a birnin Landon a ranar Litinin.

Kane ya lashe kyautar ne biyo bayan gagarumar nasarar da ya samu a kakar wasan 2025/2026 sakamakon zura ƙwallaye a raga masu yawa a matakin ƙungiyarsa Bayern, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin ‘yan wasan da ake sa ran za su lashe kyautar. Taron, wanda aka gudanar a ɗakin taro na London Palladium, yasamu halartar fitattun mutane a harkar ƙwallon ƙafa domin taya murna ga ƙwarewar ‘yan wasan da suka yi fice a ɓangaren maza da mata a harkar.

Wannan babbar nasara ce a tarihin ƙwallon ƙafar ɗan wasan, sannan hakan ya sanya shi a sahun ‘yan Ingila da suka taɓa lashe kyautar. Gabanin ya lashe, an samu irin su Stanley Matthews, Bobby Charlton, Kevin Keegan da Michael Owen da suka lashe kyautar a baya, inda Owen ne ɗan ƙasar da ya lashe ta ƙarshe a shekarar 2001.

A ɓangaren mata, Alexia Putellas ce ta lashe Ballon d’Or ta bana, wanda ke nuna ta samu ƙarin nasarori kan waɗanda ta samu a baya. Putellas ta yi nasarar ne sakamakon gagarumar gudunmawa da ta bayar a kakar wasan 2025/2026 da ƙungiyarta Barcelona a ƙasar Sifaniya wajen samun nasarori kana daga bisani ta koma ƙungiyar Ingila, wato London City Lionesses a Yuli. Wannan ya sa ta zama cikin fitattun ‘yan ƙwallon ƙafa mata da suka samu manyan nasarori a tarihi.

Matashin ɗan wasan gaba na Barcelona kuwa, Lamine Yamal, ya lashe kyautar Men’s Young Talent of the Year award, bisa nuna hazaƙa a fagen fafatawa. Kociyan Sifaniya Luis de la Fuente shi ne kocin da ya lashe kyautar ‘Men’s Coach of the Year’, yayin da kocin Barcelona, Pere Romeu ya karɓi kyautar ‘Women’s Coach of the Year’.

Ɗan wasan gaba na Arsenal Bukayo Saka, ya samu kyautar ‘Socrates Award’ bisa fice wajen taimakon al’umma ta hannun ƙungiyar BigShoe, wadda ke samar da tallafin magani ga yaran da ke buƙata. Ana bayar da wannan kyauta ne ga ‘yan wasan da suke amfani da shahararsu wajen ayyukan jinƙai da inganta rayukan al’ummar yankunansu. Burna Boy ne ya gabatar masa da kyautar bayan ya yi tsokaci kan ƙoƙarinsa ga ci-gaban harkar ƙwallon ƙafa a Nijeriya ta makarantarsa ta horar da ƙwallon ƙafa.

By Babaji

Leave a Reply