Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
An yi tambihi da kakkausar murya ga ‘yan siyasa da su daina zage-zagen juna da cin-fuska da shafa ma juna kashin kaji.
A maimakon haka, an buƙace su da su gudanar da siyasar girmamawa da martaba, ta hanyar yi ma jama’a bayanai na hanyoyin da za su bi su inganta rayuwar al’umma.
Shugaban kwamitin dattawa na jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Sani Hukuma Zauro, Zannan Gwandu, ya bada wannan shawarar a zantawar da ya yi da manema labarai a Zauro ranar Lahadi.
Zanna ya nuna rashin jin daɗi dangane da yadda ‘yan adawa ke amfani da kalamai da basu dace ba.
Ya ce masu maganar ɓatanci ga Gwamnan Kebbi, Kwamred Nasir Idris, su san da cewar bai rageshi da komi ba, fa ce, ƙara masa daraja da ɗaukaka ya yi.
Zanna ya cigaba da cewar, Gwamna Nasir Idris mutum ne mai tausayi da kyautatawa jama’a, wanda ya yi aikin raya al’umma, kuma ya cancanta a bashi goyon baya ya yi zango na biyu, a zaɓe shi ya koma mulki a zaɓen 2027.
