Kasashen Waje

Guterres ya yi gargaɗi kan AI a jawabinsa na bankwana da jagorancin Majalisar Dinkin Duniya

Guterres ya yi gargaɗi kan AI a jawabinsa na bankwana da jagorancin Majalisar Dinkin Duniya

Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin Duniya, Mista António Guterres, ya yi amfani da jawabinsa na ƙarshe a gaban Babban Taron Majalisar ɗinkin Duniya wajen yin kira ga ƙasashen duniya su ƙara tsaurara tsarin kula da fasahar AI tare da kawo ƙarshen yaƙe-yaƙen da ke ci gaba da haddasa asarar rayuka. Guterres, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 31 ga Disamba, ya ce duniya na fuskantar haɗuwar barazana daga yaƙe-yaƙe, sauyin yanayi, ƙaruwar rashin daidaito da kuma saurin bunƙasar fasahar AI, yayin da tsarin haɗin gwiwar ƙasashen duniya ke fuskantar matsin lamba.  Ya yi kira da a samar da tsarin ƙasa…
Read More
Babban ladani a masallacin Harami, Sheikh Al-Madani ya rasu

Babban ladani a masallacin Harami, Sheikh Al-Madani ya rasu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sheikh Ibrahim bin Adel Al-Madani, ɗaya daga cikin masu kiran sallar Asuba da sauran salloli a Masallacin Harami da ke Makkah, ya rasu a safiyar Litinin yana da kimanin shekaru 51. Tashar Al-Ekhbariya ta Saudiyya ce ta tabbatar da rasuwar, lamarin da ya janyo ɗimbin saƙonnin ta’aziyya da addu’o’i a shafukan sada zumunta. Al-Madani na daga cikin manyan masu kiran salla da ke aiki a Masallacin Harami. A kowace rana, mutum shida daga cikinsu ne ke yin kiran salla a jere domin sallolin farilla biyar, da kuma kiran farko na sallar Asuba, wato Assalatu An fi…
Read More
Trump ya yi barazanar ‘dulmiyar’ da Iran idan ba a cimma yarjejeniya ba

Trump ya yi barazanar ‘dulmiyar’ da Iran idan ba a cimma yarjejeniya ba

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa kasarsa za ta iya dulmiyewa ko ‘halaka’ gwamnatin Iran idan har ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ba, a wani jawabi da ya gabatar a gaban taron Majalisar ɗinkin Duniya a birnin New York ranar Talata. Trump ya ce yana da “babban hukunci” da zai yanke kan ko Amurka za ta cimma yarjejeniya da Iran, ko kuma ta ci gaba da kai mata hare-hare. Ya kuma ce ya yi imanin cewa akwai yiwuwar a cimma matsaya tsakanin Washington da Tehran.  Ya kuma zargi Iran da jan ƙafa wajen tattaunawar da za ta…
Read More
Amurka da Denmark sun ƙulla yarjejeniyar tsaron Greenland

Amurka da Denmark sun ƙulla yarjejeniyar tsaron Greenland

Amurka, Denmark da Greenland sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar tsaro da za ta ba Amurka damar faɗaɗa kasancewar sojojinta a Greenland, bayan watanni ana takaddama kan makomar yankin da ke ƙarƙashin mulkin Denmark. Shugaban Amurka Donald Trump, Firaministar Denmark Mette Frederiksen da Firaministan Greenland Jens-Frederik Nielsen ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a gefen taron Majalisar ɗinkin Duniya a New York ranar Talata.  Yarjejeniyar ta tanadi yiwuwar kafa wasu sabbin sansanonin sojin Amurka guda biyu a Greenland, tare da samar da tsarin kariya daga makamai masu linzami da Amurka ta kira “Golden Dome”. Matakin ya zo ne bayan dogon…
Read More
Kotun Sri Lanka ta ɗaure mutane 15 kan harin Easter na 2019

Kotun Sri Lanka ta ɗaure mutane 15 kan harin Easter na 2019

Wata babbar kotu a Sri Lanka ta samu mutane 15 da laifin hannu a harin kunar bakin wake da aka kai a ranar Easter ta 2019, wanda ya kashe sama da mutane 260 tare da jikkata ɗaruruwan wasu. Harin na 21 ga Afrilu 2019 ya shafi majami'u uku da manyan otal-otal uku a sassan ƙasar, lamarin da ya zama ɗaya daga cikin hare-haren da suka fi muni a tarihin Sri Lanka tun bayan kawo ƙarshen yakin basasa na ƙasar.  Rahotanni sun ce 15 ɗin an same su da hannu wajen shirya ko taimakawa waɗanda suka kai harin, yayin da wasu…
Read More
An harbe mutane 11 kusa da makaranta a Turkiyya

An harbe mutane 11 kusa da makaranta a Turkiyya

Akalla mutane 11 ne suka jikkata bayan wani ɗan bindiga ya buɗe wuta kusa da wata makarantar sakandare a birnin Turgutlu da ke lardin Manisa a yammacin Turkiyya. Hukumomin ƙasar sun ce biyu daga cikin waɗanda suka jikkata suna cikin mawuyacin hali bayan harin da ya faru ranar Talata. An kuma kama wanda ake zargin bayan harin.  Rahotanni sun ce wanda ake zargin ɗalibi ne a makarantar, ko da yake binciken hukumomi kan ainihin abin da ya kai ga harin na ci gaba. Harin ya sake dawo da hankalin jama'a kan matsalar hare-haren bindiga a makarantu a Turkiyya, bayan wasu…
Read More
Trump da Xi za su sake zama kan kasuwanci da fasahar AI

Trump da Xi za su sake zama kan kasuwanci da fasahar AI

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Chana Xi Jinping za su sake zama domin tattaunawa a Washington a wannan makon, yayin da ƙasashen biyu ke ci gaba da fafatawa kan kasuwanci, fasahar zamani da kuma ƙirƙirar basirar ɗan adam, wato AI. Ziyarar Xi da ta fara ranar Laraba, 23 ga Satumba, za ta kasance wata muhimmiyar ganawa tsakanin shugabannin manyan ƙasashe biyu masu ƙarfin tattalin arziki, a daidai lokacin da dangantakar Washington da Beijing ke fuskantar sabbin rikice-rikice kan fasaha da kasuwanci.  A cikin batutuwan da ake sa ran za su mamaye tattaunawar akwai cinikayya, harajin kaya, fitar da…
Read More
Amurka za ta gana da Rasha a New York kan rikicin Ukraine

Amurka za ta gana da Rasha a New York kan rikicin Ukraine

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio zai gana da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov, a birnin New York, a daidai lokacin da shugabannin ƙasashen duniya ke taruwa domin taron Majalisar ɗinkin Duniya. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ce ta tabbatar da ganawar, wadda za ta gudana a gefen taron Babban Taron Majalisar ɗinkin Duniya. Reuters ta ruwaito cewa ganawar za ta kasance ta farko tsakanin manyan jami’an diflomasiyyar ƙasashen biyu tun bayan ganawar da suka yi a baya.  Ganawar ta zo ne yayin da yaƙin Rasha da Ukraine ke ci gaba, tare da ƙoƙarin ƙasashe daban-daban na ganin an samu hanyar…
Read More
Guguwar Dujuan ta yi sanadin salwartar rayuka da dukiya a Japan

Guguwar Dujuan ta yi sanadin salwartar rayuka da dukiya a Japan

Akalla mutane huɗu sun mutu, yayin da wasu shida suka ɓace bayan guguwar Dujuan ta ratsa sassan Japan, inda ta haddasa ruwan sama mai ƙarfi, zabtarewar ƙasa da katsewar wutar lantarki a yankunan da ke kusa da Tokyo. Hukumar kula da gobara da bala’o’i ta Japan ta ce mutane uku sun mutu a yankin Chiba, yayin da mutum ɗaya ya mutu a Kanagawa, dukkansu yankunan da ke kusa da Tokyo. Hukumomi kuma na ci gaba da neman mutane shida da ake kyautata zaton sun ɓace bayan zabtarewar ƙasa.  Fiye da gidaje 45,000 ne suka kasance ba tare da wutar lantarki…
Read More
‘Yan sandan Congo sun tarwatsa zanga-zangar adawa da sauyin kundin tsarin mulki

‘Yan sandan Congo sun tarwatsa zanga-zangar adawa da sauyin kundin tsarin mulki

Rikicin siyasa ya sake kunno kai a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, inda ‘yan sanda suka tarwatsa zanga-zangar da masu adawa da gwamnati suka gudanar a birane da dama, domin nuna rashin amincewa da sauye-sauyen kundin tsarin mulkin kasar da ake takaddama a kansu. A babban birnin kasar, Kinshasa, daruruwan mutane ne suka fito ranar Talata domin nuna adawa da sauye-sauyen, inda lamarin ya fara cikin lumana kafin daga bisani ya rikide zuwa arangama tsakanin masu zanga-zangar da magoya bayan gwamnati. Shaidun Reuters biyu da ke wurin sun ce ɓangarorin biyu sun rika jifan juna da duwatsu tare da daga adduna, abin…
Read More