Firaministan Haiti ya kama hanyar murabus saboda matsin lambar ‘yan daba

Firaministan Haiti Ariel Henry ya yada ƙwallon mangoro domin hutawa da ƙuda, wajen miƙa murabus ɗinsa a matsayin shugaban ƙasar da ke yankin Caribbean, bayan cimma matsaya da ƙungiyar ƙasashen yankin a matsayin mafita na warware rikicin siysar ƙasar.

Shugaban ƙungiyar ƙasashen yankin Caribbean kuma shugaban ƙasar Guyana Irfaan Ali, wanda ya tabbatar da shirin murabus din Henry, ya yaba da matakin da ya kira wata dama ta kafa kwamitin shugaban ƙasa na riqon ƙwarya wanda zai naɗa firaministan riƙon kwarya.

Henry mai shekaru 74 wanda ke riƙe da kujerar firanministan Haiti da ba zaɓen sa aka yi ba tun shekarar 2021, ya tafi Ƙasar Kenya a ƙarshen watan da ya gabata domin tabbatar da jagorancin tawagar tsaro ta ƙasa da qasa da Majalisar Ɗinkin Duniya ke marawa baya don taimaka wa ‘yan sanda yaƙi da ‘yan fashi da makami, kafin dawowarsa gida ne rikicin neman murabus ɗinsa ya ɓarke tare da mummunan tashin hankali a babban birnin ƙasar Port-au-Prince abin da ya tilasta masa maƙalewa a yankin Amurka na Puerto Rico.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin yankin suka gana da safiyar Litinin a Ƙasar Jamaica da ke kusa da ƙasar, domin tattaunawa kan tsarin miqa mulki a siyasance, wanda Amurka ta buqaci a gaggauta, daidai lokacin da wasu qungiyoyi ‘yan daba ke kira ga Henry ya yi murabus.