Iyalai da almajiran Malam Mai Siddi sun yi addu’ar cika shekara 32 da rasuwarsa a Gombe

Spread the love
  • Ya bada gudunmawa wajen haɗa kan al’umma ta vangaren karatun Ishiriniya

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

A ranar Juma’ar da ta gabata ne 26 ga watan Afrilu 2024 iyalai da almajiran Sheikh Abubakar Siddi Bolari (Mai Ishiriniya) suka gabatar da addu’o’i na musamman don cika shekara 32 da rasuwarsa.


Shi dai Sheikh Malam Abubakar Siddi Mai Ishiriniya Malamin addinin Musulunci ne da ya bada gudunmawa sosai wajen ciyar da addinin Islama gaba, a tsawon rayuwarsa wanda ya bar giɓi mai wuyar cikewa.

Tarihin rayuwarsa
Sheikh Abubakar ɗa ne ga ɗan Abdullahi ɗan Salihu wanda yake jinin sharifai ne da ke da dangantaka da Sayyidina Hussain ɗan Iman Aliyu ta wajen matarsa Fatima ‘yar Manzon Allah.

Shehin Malamin da ake wa laƙabi da Ka’idun Bilkhairi, wanda ya sa masa wannan laƙabi shi ne Sheikh Bala Mai Yafe Kano, saboda yadda yake haɗa kan masoya Manzon Allah a garin Gombe da kewaye a ta dalilin karatun Ishiriniya.

An haifi Malam Siddi ne a garin Tsafe ne a Ƙaramar Hukumar Musawa a jihar Katsina a cikin shekarar 1941 ya kuma fara karatunsa ne a wajen mahaifinsa Sayyadi Abdullahi Salihu a garin Salihawa da ke ƙaramar hukumar ta Ɗan Musa a jihar ta Katsina.

Bayan rasuwar mahaifinsa sai ya koma wajen Alaramma Malam Muhammadu Kebe da ke zaune a gidan Yari Yan Doka a garin Zari’a da ya kammala karatun Alƙur’ani sai ya ci gaba da karatun littatafai na Ilimi a wajen Sheikh Malam Na’iya a garin na Zariya.

Dawowarsa Gombe
Malam Siddi Mai Ishiriniya, ya dawo Gombe ne a shekararar 1960 a wajen Baffansa Malam Sulaiman Ladan wanda ya kafa wani gari da ake ce masa garin Ladan a tsakanin ƙauyen Dumbu da Tsando a yankin ƙaramar hukumar Yamaltu Deba a jihar Gombe.

Inda a shekarar 1966 kuma ya baro can garin na Ladan ya dawo cikin garin Gombe ya ci gaba da karatu a wajen Sheikh Saleh Dan Sadauki da ke unguwar Bolari a fadar jihar Gombe.

Gudumawarsa wa addini
Har ila yau a wannan shekara ta 1966 sheikh Mai Ishiriniya ya buɗe wata Makaranta ta karatun Alkur’ani da sauran bangarorin Ilimi a Gidan sa da inda Makarantar ta samu karbuwa saboda kyakkyawar tsarin da aka yi mata wanda yake kama da tsarin Makarantar Boko ta gwamnati.

A shekarar 1971 sai wani Attajiri mai suna Alhaji Danlami Mai Kwano ya gina musu wani waje na daban saboda ganin yadda Makarantar ta tara Dalibai masu yawa sai aka sawa Makarantar sunan shi wannan Attajiri wato Madarasatul Danlami Islamiyya saboda karrama shi bisa wannan ƙoƙari da ya yi na gina wajen karatun na daban da dukiyarsa.

Ana haka da ƙungiyar Fityanul Islam ta bude reshen ta a garin Gombe a shekarar 1975 sai ta bai wa Alhaji Ɗanlami Mai Kwano shugabanci sai aka sanya makarantar a tsari irin na makarantun Fitynaul Islam.

A shekarar 1984 kuma sai Fityanul Islam ta yiwa Makarantar Rijista ta ba ta satifiket wacce ta zama ta goma sha bakwai a cikin jerin Makarantun ta a faɗin Najeriya.

Bisa irin wayewar kai da Ilimi da ake samu a wannan makaranta sai hukumar Ilimi ta karamar hukumar Gombe ta nemi a mayar da makarantar ta zama Firamare ta Boko ko kuma Islamiyya da firamare, inda suka tura musu wasika a lokacin Marigayi Alabura S Kudi yana Sakataren Ilimi, amma ganin idan aka mayar da Makarantar ta zama Firamare an takaita ilimin da ake samu na addini sai shi Malam Siddi ya ce hakan ba zai yiwu ba a koma tsari irin na farko wato na addini tsantsa.

Sheikh Malam Siddi, bai tsaya iya nan ba ya sake buɗe Makaranta ta Manya zalla dan karatun addini na alƙur’ani da littatafan ilimi wanda ita ma makarantar ta samar da wadanda suka dinga yiwa addini hidima tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu.

Ganin yadda Sheikh Malam Siddi ya yiwa addini hidima yasa bayan rasuwar sa da shekara 32 iyalan sa da Alamjiran su suka shirya taron addu’a na musamman wanda ba’a taba yin irin sa ba don tuna irin ayyukan alkhairi da ya yi tare da wasu manyan dattawan unguwar Bolari da suka rasu daga wancan lokacin zuwa yanzu da aka gudanar a ranar Juma’a 26 ga watan Afirilu 2024 a makarantar ta Madarasatul Ɗanlami Islamiyya da ke Bolari.

Taron addu’ar ya samu halartar manyan shehinnan Ɗarika da alarammomi da almajiran Shiekh Malam Siddi Mai Ishiriniya da sauran su inda aka masa addu’oi sosai tare da manyan Dattawan Unguwar Bolari da suka rasu a bayan sa.
Sheikh Malam Siddi Mai Ishiriniya, ya rasu shekaru 32 da suka gabata ya bar ‘ya’ya da dama cikin su har da Sharu Auwal Siddi Bolari Garkuwan Sharifan Gombe Talban Sharifan Najeriya da Sharu Sani Siddi, da Sharu Salisu Siddi Ka’idun Bilkhair kuma shugaban kungiyar Fityanul Islam na ƙaramar hukumar Gombe sannan kuma Tafidan Sharifan Najeriya, sai Sharu Khamisu Abubakar Siddi Gusau Wazirin Larabawan Sharifan Gusau, da Tasiu Siddi Shugaban Anwarul Faida na ƙaramar hukumar Yamaltu Deba sai kuma Sharu Sabi’u Siddi Shugaban Anwarul Faida Wuro Gaini na karamar hukumar Akko.

Babban ɗan Marigayin Sharu Auwal Siddi Bolari, Garkuwan Sharifan Gombe ya nuna farin cikin sa da kuma jin dadi na yadda almajiran Mahaifin su suka hada kai da su wajen ganin an gudanar da wannan taron addu’a domin tunawa da mahaifin su bayan rasuwar sa da shekara 32.

Sharu Auwal Siddi, ya kuma kirayi al’ummar musulmi musamman masu hannu da shuni da cewa su dinga aikata ayyukan alkahiri da za’a yi koyi da su wata rana a tuna su a musu addu’a kamar yadda yanzu aka yi wa mahaifin su da wasu Dattawa saboda gudumawar da ya bayar a rayuwar sa lokacin da yake raye.

Daga nan sai ya ce ba su da wata kalma ta godiya ga ɗimbin al’umma da suka halarci taron addu’ar sai dai kawai fatan alkhairi da musu fatan Allah ya biya su da mafificin alkhairi.

By Editor