Daga BASHIR ISAH
Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Kano ta ba bai wa Hukumar Kula da Wutar (NERC) da kamfani Kano Electricity Distribution Company (KEDCO) kan kada su aiwatar da ƙarin kuɗin wutar lantarkin da aka yi ga masu amfani da wutar lantarki na Band A.
Kwanankin bayana ne NERC ta umarci kamfanonin rarraba wutar lantarki da su ƙara kuɗin wutar da suke bai wa kostomominsu na rukunin Band A domin samun wadatar wutar lantarki.
Sai da daman ‘yan Nijeriya sun soki matakin na NERC musamman yadda hukumar ta ɗora da yawan kostomomin nata a tsarin Band A duk da haka ba a samun wutar kirki.
Sai dai Alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Kano, A.M. Liman ya bai wa NERC umarni kan a dakatar da aiwatar da ƙarin kuɗin wutar biyo bayan ƙarar da lauya A.B. Mahmoud, SAN, ya shigar.
Mahmoud ya shigar da ƙarar ne a madadin kamfanonin da suka haɗa da Super Sack Company Limited da BBY Sacks Limited da Mama Sannu Industries Limited da Dala Foods Nigeria Limited da Tofa Textile Limited da kuma Manufacturers Association of Nigeria Limited (MAN).
Umarnin kotun ta taka wa NERC da kamfanin KEDCO burki daga barin aiwatar da ƙarin kuɗin wutar wanda aka tsara ya fara aiki daga wannan watan.
