Daga BASHIR ISAH
Shugaban Hukumar Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa, ya sanar da bai wa ‘yan jarida gurbi guda 50 a shirin auren zawarawan da hukumar za ta yi nan gaba.
Daurawa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai ranar Laraba a Kano.
Ya ce, sako ‘yan jarida da sauransu a cikin shiri, zai taimaka wajen daɗa bunƙasa shi.
Daurawa ya ƙara da cewa, shirinta na gaba zai haɗa har da lauyoyi da ma’aikatan kiwon lafiya da sauransu.
Wannan na zuwa ne bayan da hukumar ta samu nasarar ƙulla aure 1,800 a shirin auren zawarawan da ya gabata.
Malamin ya ce, manufar shirin auren zawarar ita ce domin tsaftace al’umma da hana aikata masha’a a tsakanin matasa.
