
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS, ta kammala gabatar wa kotu hujjojinta akan shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, na tuhumar sa da laifin naɗar hirar Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu ba bisa doka ba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Mai Shari’a Joyce Abdulmalik ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙorafin neman sassauta sharuɗɗan bayar da belin El-Rufa’in daga ɓangaren masu kare shi.
A cewar Mai Shari’ar, sharuɗɗan belim masu tsauri da aka kafa tun farko za su cigaba da aiki. Sharuɗɗan sun haɗa da buƙatar masu tsaya masa su kasance manyan ma’aikatan gwamnati masu matakin daraja ta 17 tare da mallakar kadarori a yankunan Maitama ko Asokoro, da kuma takardar shaida daga Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna.
Ta bayyana cewa, har yanzu akwai mutanen da suka cancanci cika waɗannan sharuɗɗa don haka kotun ba za ta ɗauki matakin sassauta su ba.
A zaman kotun na ranar Talata, DSS ta sanar da gabatar da hujjoji a kan El-Rufai, inda ta tabbatar cewa ba za ta ƙara kiran wasu shaidu ba.
Lauyan da ke kare El-Rufai, Paul Erokoro, ya bayyana aniyarsu ta shigar da “buƙatar rashin hujja,” inda suke cewa masu gabatar da ƙara sun gaza kawo hujjoji masu ƙarfi da za su tabbatar da tuhumarsu akan tsohon gwamnan.
Daga nan ne kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Satumba, 2026, domin cigaba da hukunci akan al’amarin.
