Ministan Tsaro zai yi jawabi yayin da Blueprint ta shirya jagorantar taron karrama gwarazan ‘yan ƙasa na 2025

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanin Jaridun Blueprint ya shirya jagorantar taronsa na lakcar shekara-shekara ta 2025 da shirye-shirye da kuma bayar da lambobin yabo a Abuja, wanda ake sa ran zai haɗa jami’an gwamnati, masu samar da tsare-tsare, masana harkar difulomasiyya, jagororin tsaro, ‘yan majalisar dokoki, shugabannin masana’antu, malamai, ƙungiyoyin al’umma, abokan hulɗar samar da ci-gaba da sauran masu ruwa da tsaki.

Manhaja ta ruwaito cewa, an shirya gudanar da taron ne a ranar Talata, 18 ga Agusta, 2026, a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu, wanda za a fara da misalin ƙarfe 10:00 na safe.

Taron zai bayar da damar samar da fagen tattaunawa kan al’amuran da suka shafi ƙalubalen tsaro da martabar babban zaɓen shekarar 2027 da ke tafe domin gudanar da shi bisa gaskiya da adalci.

Takardar gayyata zuwa taron na ɗauke ne da sanya hannun Darakta Manaja kuma shugaban Blueprint Newspapers Limited, Salisu Umar a madadin hukumar gudanarwar kamfanin.

A taron na wannan shekarar, za a samu muhimmin jawabin gabatarwa daga Mai Girma Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin (mai ritaya), wanda zai yi magana akan ƙalubalen tsaro da zaɓukan 2027 mai taken “Security Challenges and the Integrity of Nigeria’s 2027 Elections”.

Blueprint ya ce taron nasa na shekara-shekarar ya zama ɗaya daga cikin muhimman fagagen Nijeriya wajen ƙara wa juna sani akan al’amuran da suka shafi muhimmancin ƙasa, samar da fage ga manyan masu ruwa da tsaki don musayar shawarwari da yin nazari akan lamuran da za su taimaka wajen samar wa Nijeriya gobe mai kyau.

A cewar masu shiryawa, za a bayar da lambobin yabo ne da nufin karrama ƙwarewa da gudummawar hidimta wa al’umma, samar da ci-gaba a fannin tattali, ƙirƙira da kuma shugabanci na gari.

Kamfanin ya kuma ce, bayyanar waɗanda aka gayyata a taron za ta ƙara masa daraja, inda ya bayyana hakan a matsayin tattaunawa kan muhimmancin ƙasa da murnar bikin ƙwarewa.

Kazalika, ana sa ran taron ya mayar da hankali akan alaƙar da ke tsakanin tsaro da sahihin zaɓe, yayin da kuma za a yi nazari kan lamuran kare darajar hanyoyin gudanar da zaɓe da kuma goben dimukraɗiyyar Nijeriya.

By Babaji

Leave a Reply